‘Yar Asalin Jihar Kogi Ta Lashe Gasar Wacce Tafi Kowa Kyawun Fuska A Najeriya A 2022

‘Yar Asalin Jihar Kogi Ta Lashe Gasar Wacce Tafi Kowa Kyawun Fuska A Najeriya A 2022

  • Wata matashiya mai suna Deborah Isa ta yiwa sa'anninta zarra wajen lashe gasar sarauniyar kyau
  • Deborah wacce haifaffiyar yar jihar Kogi ce ta lashe gasar wacce tafi kowa kyawun fuska a Najeriya wanda aka yi a karo na tara
  • An gudanar da taron a jihar Lagas inda ta samu kyautar babban mota kuma za ta wakilci Najeriya a gasar sarauniyar kyau na kasa da kasa

Lagas - Budurwa ‘yar shekaru 20, Isa Deborah ta doke sauran takwarorinta wajen lashe gasar wacce tafi kowa kyawun fuska a Najeriya a 2022.

Taron wanda shine karo na tara ya gudana ne a wajen hada sautin kida na Koga da ke yankin Ikeja ta jihar Lagas a ranar 27 ga watan Agusta kuma kamfanin Zanzy Entertainment ne ya dauki nauyinsa.

Kara karanta wannan

Hotuna da Bidiyon shagalin Gaɗa da aka yi na bikin Gimbiya Ruƙayya Bayero

Deborah Isa
‘Yar Asalin Jihar Kogi Ta Lashe Gasar Wacce Tafi Kowa Kyawun Fuska A Najeriya A 2022 Hoto: LIB
Asali: UGC

Deborah dai ta mallaki digiri a bangaren zamantakewa daga babbar jami’ar Abuja kuma ta kasance haifaffiyar karamar hukumar Kabba/Bunu a jihar Kogi.

Matasgiyar na son girki, tafiye-tafiye, buga wasan kwallon tebur da sauransu, bata kaunar munanan dabi’a da rashin adalci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shafin LIB ya kuma rahoto cewa matashiyar budurwar za ta aiwatar da wani aikinta wanda zai karkata ne a kan mata da yara a garinta da Najeriya baki daya.

A cewar shugaban gasar ta wacce tafi kyawun fuska a Najeriya, Mista Chuks Anusionwu, wanda ya gabatar mata da dankarareiyar motar da ta lashe a taron, Deborah za ta kuma jagoranci Najeriya a gasar kyawun na kasa da kasa.

Yadda Budurwa Ta Zama Mai Goge-goge Bayan Kammala Digiri Na Biyu, Allah Ya Sauya Rayuwarta A Karshe

A wani labarin, wata matashiyar budurwa da ta gaza samun aiki mai kyau bayan kammala karatunta ta bayyana cewa ta shiga damuwa a saboda haka. Bayan dan wani lokaci, ta fara aiki a matsayin mai goge-goge duk da cewar tana da digiri biyu.

Kara karanta wannan

Zan Siya Gida Kwanan nan A Birnin Lagas: In ji Mai Sana’ar Kifi, Mutane Sun Karfafa Mata Guiwa

Daga nan sai ta fara koyawa wasu dalibai yadda za su yi addu’a da azumi. Budurwar tana kuma karantar da su darusa daga littafi mai tsarki.

Duk da wannan hali da take ciki da kuma kasancewarta mai goge-goge, ta yi tawakkali da Allah sannan ta ci gaba da koyar da kananan yara a hanya madaidaiciya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel