Dangote Ya Haura Matakai Hudu Amma Ya Tafka Asarar N10.4bn a Wata Daya

Dangote Ya Haura Matakai Hudu Amma Ya Tafka Asarar N10.4bn a Wata Daya

  • Hamshakin attajirin Najeriya da Afirka, Aliko Dangote ya tsallake matakai hudu a teburin attajirai da aka fitar a baya-bayan nan
  • Sai dai matakin bai kara masa komai a arzikinsa ba domin kuwa, attajirin ya ma tafka wata asara ce ra kimanin Naira biliyan 10.4 a cikin wata guda
  • A bangare guda, hamshakin attajirin kasar India, Gautam Adani ya zama mutum na uku a jerin attajirai, inda ya maye gurbin Bill Gates a watan da ya gabata

Duk da tsallake matakai hudu a teburin hamshakan attajirai, hamshakin mai kudin Najeriya, Aliko Dangote, ya tafka asarar kudi kimanin Naira biliyan 10.4 daga dukiyarsa.

A sabon jadawalin Bloomberg na kwana-kwanan nan, Dangote ya hau matsayi na 76 a jeren, inda ya tsallake matakai har hudu daga inda yake a baya; na 80 - a watan da ya gabata, amma dai hakan bai kare shi da komai ba ta fuskar karin arziki.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wani kasurgumin dillalin bindiga dauke da makamai zai tafi Zamfara

Irin asarar da Dangote ya tafka, amma ya kara matsayi a attajiran duniya
Dangote Ya Haura Matakai Hudu Amma Ya Tafka Asarar N10.4bn a Wata Daya | Hoto: cnbcfm.com
Asali: UGC

Simintin Dangote ya fadi

Hamshakin da ya fi kowa kudi a Afirka ya tafka asarar zunzurutun kudi har Naira biliyan 10.4 saboda faduwar kason kamfaninsa na siminti.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kididdigar ta Bloomberg ta shekara zuwa yau ta nuna gibin dalar Amurka miliyan 15.3 daga dukiyar hamshakin attajirin - wanda ke nuni da tafka asara a watan jiya; Agusta.

A bangare guda, wani abin mamaki ya faru, yayin da hamshaki Gautam Adani na Indiya ya zama mutum na uku mafi kudi a duniya, bayan Elon Musk da Jeff Bezos.

Adani dai shi ne mamallakin kamfanin Adani Group, wani kamfani a India dake harkallar jiragen ruwa, rarraba wutar lantarki, makamashi da jiragen sama.

Adani ya kulla yarjejeniyar makamashi

Kamfanin Adani ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya da TotalEnergies don hada gwiwa a fannin makamashi.

An ce dai Adani korarre ne daga makaranta kuma shi ya yiwa mai kamfanin Microsoft, Bill Gates fintinkau a jerin attajirai a watan da ya gabata

Kara karanta wannan

Barayin Mai: Gwamnati Ta Kawo Hujjar Ba Tsohon Tsageran N/Delta Kwangilar N48bn

Rahotanni daban-daban sun bayyana cewa, dukiyarsa ta karu da akalla dala biliyan 60 a bana.

Hannun jari: Yadda kamfanin sukarin Dangote ya rage daraja da kusan N11bn saboda rikici da BUA

A wani labarin, rikici tsakanin kamfanin BUA da na sukarin Dangote ya zama mai girma a masana'antar sukari, kuma alamu na nuna tafiyar ta fi karbar BUA wanda ya zargi kamfanin sukarin Dangote kwanan nan da son haifar da karancin sukari.

A cinikayyar ranar Laraba, 23 ga Fabrairu, 2022, farashin hannun jarin kamfanin sukarin Dangote ya ragu da 5.28%, inda kasuwa ta rufe yana da Naira 17.05 kan kowane hannu, farashin kasuwarsa ya sauka kenan daga Naira biliyan 218 zuwa Naira biliyan 207.10.

Kamfanin sukarin ya sami raguwar farashin hannun jari, kuma za a iya danganta shi da sauyin ra'ayin masu zuba hannun jari wanda ya haifar da sayar da hannayen jari a kamfanin kan kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Osinbajo ya shiga batun ASUU, ya fadi abin da gwamnati za ta yi

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.