Hotunan Jana'izar Mutune 7 Yan Gida Ɗaya Da Suka Rasu Bayan Sunyi Karin Kumallo Da Dambu A Sokoto

Hotunan Jana'izar Mutune 7 Yan Gida Ɗaya Da Suka Rasu Bayan Sunyi Karin Kumallo Da Dambu A Sokoto

  • Mutanen kauyen Kaura da ke karamar hukumar Yabo ta Jihar Sokoto sun shiga jimamin rashin wasu mata 2 da yayansu biyar da suka rasu
  • Rahotanni ya nuna cewa daya cikin matan ne ta dafa dambu dukkan yan gidan suka ci yayin karin kumallo amma daga bisani suka fara ciwon ciki wanda ya yi sanadin rasuwarsu
  • Malam Danbala, mijin matan biyu da yaran biyar ya bayyana yadda labarin bakin cikin ya iso masa a lokacin yana jihar Neja inda ya ke aiki

Jihar Sokoto - Wani abin bakin ciki ya faru a kauyen Kaura da ke karamar hukumar Yabo ta Jihar Sokoto a yayin da mutane bakwai yan gida daya suka mutu bayan yin karin kummalo.

Mai gidan, Malam Danbala ya shaida wa Daily Trust cewa ya rasa matansa biyu da yaransa biyar sakamakon afkuwar lamarin.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Bude Baki Kan Gaskiyar Abin da Ya Faru Da Su da Shekarau a NNPP

Jana'iza Sokoto
Matan Aure 2 Da Yaransu 5 Sun Mutu Bayan Yin Karin Kumallo A Sokoto. Hoto: @lindaikeji.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Ina jihar Neja inda na ke aikin leburanci lokacin da dan uwa na ya kira ni a waya ya ce akwai matsalar da ya faru kuma ana bukatan in dawo gida cikin gaggawa.
"Ya bukaci in yi gaggawa in dawo. Na tambaye shi abin da ya faru amma ya katse kiran ba tare da ya bani amsa ba.
"Na shigo motar asubu zuwa Sokoto, na tarar dukkan iyalai na sun mutu sai yar karamar yarinya daya. An birne su kafin in dawo ranar Talata kamar yadda addinin mu ya koyar."

Yadda abin ya faru

Danbala ya ce matsalar ta samo asali ne lokacin da daya cikin matansa ta dafa dambu da safe.

Magidancin ya ce:

"Dukkansu sun ci sun koshi amma bayan wani lokaci suke fara cewa cikinsu na ciwo kuma aka garzaya da su abiti.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Matashi Ya Sha Mamaki Bayan Yara Mabarata Sun Tara Masa Kudin Siyan Abinci Bayan Ya ce Yana Jin Yunwa

"Yaran biyar suka fara mutuwa, sai matan nawa guda biyu amma karamar yarinyar tana samun sauki saboda bata ci da yawa ba."

Ya ce abin da ya faru kaddara ne daga Allah kuma ya yi addu'ar Allah ya saka musu da gidan aljanna Firdausi.

Ganau ya magantu

Wani da abin ya faru a idonsa ya ce da farko matar ta fara dafa dambun ne da daren ranar Lahadi kuma ta raba wa makwabta.

An ce ta ajiye ragowar abincin don su ci da safiyar ranar Litinin, ta hada sauran abin da wani danyen dambu da aka bari ya kwana a bude. Ta dafa abincin amma mutanen gida kawai ta bawa.

Ga Hotunan yadda aka yi jana'izar wadanda suka rasu

Jana'iza Sokoto
Matan Aure 2 Da Yaransu 5 Sun Mutu Bayan Yin Karin Kumallo A Sokoto. Hoto: @lindaikeji.
Asali: Twitter

Jana'iza Sokoto
Matan Aure 2 Da Yaransu 5 Sun Mutu Bayan Yin Karin Kumallo A Sokoto. Hoto: @lindaikeji.
Asali: Twitter

Jana'iza Sokoto
Matan Aure 2 Da Yaransu 5 Sun Mutu Bayan Yin Karin Kumallo A Sokoto. Hoto: @lindaikeji.
Asali: Twitter

Makabar
Makbarta da aka birne wadanda suka rasu. Hoto: @lindaikeji.
Asali: Twitter

Mai gida, matarsa, yarsu da 'yar aikin su duk sun mutu bayan cin abinci mai guba

A wani rahoton, babban tashin hankali ya barke a Ugbo Paul, wani yanki na Abakpa Nike da ke Enugu ta gabas a cikin jihar Enugu bayan mutane 3 tare da mai mu su hidima sun kwanta dama bayan cinye wani abinci da ake zargin ya na dauke da guba.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Osinbajo ya shiga batun ASUU, ya fadi abin da gwamnati za ta yi

Jaridar The Punch ta ruwaito yadda jaririyar su mai watanni 9 ce kadai ta tsira sakamakon rashin cin abincin da ta yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: