Mai gida, matarsa, yarsu da 'yar aikin su duk sun mutu bayan cin abinci mai guba

Mai gida, matarsa, yarsu da 'yar aikin su duk sun mutu bayan cin abinci mai guba

  • Rudani ya barke a Ugbo Paul, wata anguwa a gabashin Enugu bayan an rasa rayuka 4 a gida daya
  • Hakan ya biyo bayan miji, mata, diyar su da mai mu su hidima sun lamushe wani abinci
  • Ana zargin guba ne a cikin abincin, sai dai yarinya mai watanni 9 ce kadai ta tsira saboda ba ta ci abincin ba

Enugu - Babban tashin hankali ya barke a Ugbo Paul, wani yanki na Abakpa Nike da ke Enugu ta gabas a cikin jihar Enugu bayan mutane 3 tare da mai mu su hidima sun kwanta dama bayan cinye wani abinci da ake zargin ya na dauke da guba.

Jaridar The Punch ta ruwaito yadda jaririyar su mai watanni 9 ce kadai ta tsira sakamakon rashin cin abincin da ta yi.

Kara karanta wannan

Jarumin Gwamna El-Rufai ya bayyana abinda ke matukar tsorata shi

Miji, mata, yarsu da 'yar aikin su duk sun mutu bayan cin abinci mai guba
Mai gida, matarsa, yarsu da 'yar aikin su duk sun mutu bayan cin abinci mai guba. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wadanda su ka rasa rayukan na su sun hada da mai gidan, Mr Lawrence Chukwu, matar sa, Chizoba, diyar su, Nazareth da kuma hadimar su, Ukamaka.

Kamar yadda ya zo a ruwayar The Punch din, makwabciyar su, Mrs Dominic Gloria ta tattauna da wakilin Punch inda ta bayyana yadda iyalan Chukwu su ka kwanta bacci a ranar Juma'a salin-alin.

Ta ce ranar Asabar ta gan su rai a hannun Allah

Kamar yadda ta bayyana:

"Mun tashi da safiyar Asabar inda mu ka gan su rai a hannun Allah. Ba mu san abinda ya same su ba. Daga nan ne aka nufi asibitin yankin 82 na sojoji da su. Can da rana mai mu su hidima ta rasu.
"Bayan gwaje-gwajen asibiti iri-iri ne aka gano cewa abincin da su ka ci kafin su kwanta da daren Juma'a ya na dauke da guba. Sai dai an yi iyakar kokarin ceto su amma abin ya ci tura, a ranar Asabar matar da mijin suka rasu. Safiyar Talata kuma diyar su mai shekaru 2 ta rasu."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun damƙe dodanni biyu kan laifin aikata fashi da makami

Mahaifiyar marigayiya Chizoba, Mrs Elizabeth Nwankwo, ta kara tabbatar wa da Punch aukuwar lamarin a ranar Talata.

Kamar yadda ta bayyana, a ranar Asabar an kira ta a waya inda aka sanar da ita mutuwar hadimar su.

Kamar yadda ta bayyana:

"Bayan na isa can ne na tarar da diya ta da mijin ta kwance rai a hannun Allah. Na dauki gawar hadimar ta na kai gidan iyayen ta, kafin in dawo na tarar diya ta da mijin ta ma sun kwanta dama. Da safiyar nan, yarinyar su da muke sa ran za ta warke ma ta kwanta dama."

Yayin da take bayani akan yadda lamarin ya faru, Mrs Nwankwo ta ce an tafi da gawar jikar ta zuwa kauyen su dake Ameta Mgbo, karamar hukumar Awgu a jihar Enugu don a birne ta, yayin da gawawwakin diyar ta da mijin su ke ma'adanar gawawwaki.

A cewar ta, asibitin ne su ka sanar da ita cewa abinci mai guba ne su ka ci kafin su kwanta bacci ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnan Kano Ganduje ya mika wa 'yar shekaru 14 mulkinsa na dan lokaci

Mrs Nwankwo ta bukaci 'yan Najeriya su tallafa ma ta wurin kulawa da jaririyar da ta tsira.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Daniel Ndukwa ya ce ba su samu wannan labarin ba. Amma ya kara da cewa:

"Zan yi bincike a kan lamarin kuma zan tuntube ku."

Har yanzu dai ba a ji komai ba daga gare shi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel