'APC Ya Ke Yi Wa Aiki': Mambobin NNPP A Kaduna Sun Bukaci A Kwace Takarar Gwamna Daga Hannun Hunkuyi
- Wasu kungiyoyin matasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, sun yi zanga-zangan neman a kwace takarar gwamna daga hannun Sanata Hunkuyi
- Kungiyoyin sun yi zargin cewa Hunkuyi yana hada kai da jam'iyyar APC mai mulki a jihar kuma ya sayar da takarsa da na sauran yan takarar jam'iyyar na NNPP
- A martaninsa, Sanata Hunkuyi ya ce daukan hayan matasan aka yi don bata masa suna kuma duk zargin da suka masa ba su da tushe kuma ba gaskiya bane
Jihar Kaduna - Hadakar kungiyoyin matasa a jam'iyyar NNPP Jihar Kaduna sun yi kira ga shugabannin jam'iyyar na kasa su canja dan takarar gwamnan jihar, Sanata Suleiman Hunkuyi.
Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wani takardar korafi da ta mika wa Ben Bako, shugaban jam'iyyar NNPP na jihar, The Cable ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ta yi ikirarin cewa Hunkuyi yana yi wa jam'iyyar APC ne aiki, ta kara da cewa har yanzu akwai damar a canja yan takara.
Takardar korafin ta ce:
"Dan takarar gwamnan mu yana da halin hawainiya na 'soyayya' da abokan hamayyar mu a jihar, mafi yawancin mabiya jam'iyyar ba su gamsu da wannan abin da ya ke yi ba don haka zai janyo mana matsala."
Takardar ta cigaba da cewa:
"Muna tsoron dan takarar mu ya riga ya sayarwa jam'iyyar APC takararsa, tunda an san shi da yaudara a tarihin siyasar Kaduna.
"A matsayinsa na dan takarar gwamna, ya kamata ya zama mai hada kan sauran yan takara, amma shi ke raba kan sauran yan takara wanda hakan cin amanar jam'iyya ne.
"Dan takarar gwamnan mu ya yi amfani da karfin ikonsa ya hana yan takarar da suka cancanta samun tikiti a zone I da zone II na jihar, ya zabi yan takara wadanda APC za ta iya kayar da su cikin sauki.
"Muna kira ga shugabannin jam'iyya su maye gurbin Sanata Othman Hunkuyi wani dan takara wanda ya fi shi nagarta a NNPP na Jihar Kaduna."
Martanin Hunkuyi kan neman a tsige shi
A bangarensa, Hukunyi ya ce wannan wasan kwaikwayo ne kawai.
Ya ce an dauki nauyin matasan ne su bata masa suna da zargin da ba a iya tabbatarwa ba.
Ya kara da cewa:
"Ba za a iya tabbatar da dukkan zargin da ake min ba, kawai so ake a kawo wa takara ta cikas, amma ina fada maka wannan barkwanci ne kuma ba zai haifar da sakamako ba".
Kwankwaso Ya Yi Martani Kan Rufe Ofishin NNPP Da Yan Sanda Suka Yi A Borno Gabanin Ziyararsa
A wani rahoton, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shuganan kasa na jam'iyyar New Nigeria People Party, NNPP, da jami'an tsaro suka yi a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta, tsohon gwamnan na Jihar Kano ya yi Allah-wadai da matakin.
Amma, duk da hakan ya yi kira ga magoya bayan jam'iyyarsu ta NNPP su kwantar da hankulansu tare da kasancewa masu bin doka da oda a yayin da suke kokarin warware matsalar.
Asali: Legit.ng