Shugaba Buhari Ya Gana da Gwamnonin Jam'iyyar APC a Aso Rock
- Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya gana kofa kulle da gwamnonin jam'iyyar APC a gidan gwamnati dake Abuja
- Har yanzu babu bayanin abinda suka tattauna a wurin taron wanda ya kwashe mintuna 30 kuma gwamnonin ba su faɗi komai ba
- Wannan taron na zuwa ne a lokacin da jam'iyyun siyasa ke cigaba da gyara ɗamara domin tunkarar babban zaben 2023
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ranar Talata, ya sa labule da gwamnonin jam'iyyar APC a fadarsa dake babban birnin tarayya Abuja.
Gwamnonin sun shiga ganawar sirri da Buhari ne ƙarƙashin jagorancin shugabam ƙungiyar gwamnonin APC (PGF) kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu.
Mai taimaka wa shugaban ƙasa ta fannin kafofin sada zumunta, Buhari Sallau, shi ne ya bayyana haka a shafinsa na dandanlin sada zumunta wato Facebook.
"Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya karɓi baƙuncin ƙungiyar gwamnonin cigaba a gidan gwamnati ranar 30 ga watan Agusta, 2022," inji Sallau yayin da ya tura Hotunan taron a shafinsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da, gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, Dakta Kayode Fayemi na jihar Ekiti, Abubakar Badaru na jihar Jigawa da gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun.
Sauran su ne; Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja, Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe, Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, Simon Lalong na jihar Filato da mataimakin gwamnan jihar Ebonyi, Dakta Eric Igwe.
Ba'a bayyana ajendar da suka tattauna a taron ba, haka zalika gwamnonin ba su yi bayani ga manema labarai ba bayan kammala taron wanda suka kwashe mintuna 30.
Hotunan taron gwamnonin da Buhari
A wani labarin kuma Bayan Shafe Watanni Ana Dako, Muhammadu Buhari Ya Rattaba Hannu a Sababbin Dokoki 8
A ranar Litinin, 29 ga watan Agusta 2022, muka ji Mai girma Muhammadu Buhari ya sa hannu a wasu kudirori takwas da yanzu sun zama dokokin kasa.
Wani jawabi da aka ji daga bakin Hon. Nasir Illa ya tabbatar da cewa wadannan kudirorin da suka zo gaban Mai girma shugaban Najeriyan sun samu shiga.
Asali: Legit.ng