Tsoffin Maza Sun Fi Iya Soyayya: Matashiya Yar Shekaru 30 Da Ta Auri Dan Shekaru 80
- Mwamini, wata mata mai shekaru 30 ta bayyana cewa ta tsinci kanta a cikin yanayi mafi dadi a rayuwarta bayan ta auri Katembela Etienne
- Tsohon mai shekaru 80 ya auri Katembela bayan masoyiyarsa ta farko ta mutu ta bar shi
- Mutuniyar kasar Kongon ta shawarci yan mata a kan kada su guji auren tsoffi domin ba za su taba yin danasani ba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kongo - Wata mata da ta dulmiya a cikin soyayya ta baiwa mutane da dama mamaki bayan ta bayyana irin soyayyar da suke sha da sahibinta, wanda zai iya yin kaka da ita.
Tazarar shekaru 50
Matashiyar wacce ta fito da Mudaka, yankin Kudancin Kivu a damokradiyyar Kongo, ta ce soyayya babu ruwansa da banbancin shekaru kuma bai da iyaka.
Tsawon shekaru biyu kenan da Mwamini ta auri burin ranta Katembela Etienne.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tazarar shekaru da ke tsakaninsu shine abun da ke ba mutane da dama mamaki domin shekawun Mwamini 30, mijinra Katembela ya bata shekaru 50, kamar yadda kafar labarai na Afrimax English ya bayyana.
Katembela ya tunkari Mwamini
Matar wacce ke da haihuwa daya ta ce Katambela ya tunkareta bayan ya shafe tsawon lokaci yana rayuwa shi kadai, bayan matarsa ta farko ta kamu da rashin lafiya sannan ta mutu.
Ya bayyana mata nufinsa cewa yana so ne ya aureta, amma sai Mwamini ta dauki lokaci wajen yin tunani kan wannan bukata tasa.
Ta yarda cewa yadda take shafe lokaci da tsohon haka ta ke jin sonsa na karuwa a zuciyarta.
Sai Katembela ya biya sadakinta sannan ya dauki Mwamini a matsayin abokiyar rayuwarsa, ya sake samun soyayya a karo na biyu.
Katembela ya ce tsoffi sun fi matasa sanin yadda ake soyayya domin sun san abun da mata ke so.
Ya kara da cewa matasa malalata ne kuma basu san yadda ake kula da mace ba; don haka, tsoffi sun fi su dadin harka.
Mutumin kasar Kongon ya kuma shawarci mutane da kada su dasa iyaka a soyayya domin za su kare da batawa mutum daya koma bangarorin biyu.
Mwamini ta goyi bayan mijinta, cewa kada yan mata su tsaya tunani da zaran dattijo ya tunkare su.
Ta ce soyayya babu ruwanta da shekaru ko kyale-kyale, wanda wasu ke tunanin shine dalilin da yasa ta auri mutumin.
Ma’auratan sun haifi da daya tare kasa da shekaru biyu bayan aurensu.
Mwamini ta ce mutane da dama suna ta tambayan dalilinta na auren Katembela amma sai tayi murmushi sannan ta wuce abunta.
Yadda Budurwa Mai Shekaru 22 Ta Fada Soyayyar Tsohon Mai Shekaru 88 Har Ta Samu Juna Biyu
A wani labarin kuma, Chibalonza ta kasance matashiya yar shekaru 22, amma kuma sai ta fada a tarkon soyayya da tsohon da ya isa yin jika da ita, wato Kasher Alphonse mai shekaru 88.
Mutumin ya fada ma Afrimax English cewa sun kasance suna son juna kuma sun fahimci junansu duk da banbancin shekaru 66 da ke tsakaninsu.
A cewar masoyan wadanda suka shafe tsawon shekaru biyu tare, sun fada a tarkon soyayya da zuciyoyinsu ne amma ba wai da shekarunsu ba.
Asali: Legit.ng