An Tsinta Gawar Ɗaliban Jami'a Masoyan Juna Tsirara a Ɗakin Kwanansu

An Tsinta Gawar Ɗaliban Jami'a Masoyan Juna Tsirara a Ɗakin Kwanansu

  • An tsinta gawar saurayi da budurwa duk daliban jami'ar jihar Kwara a dakin saurayin dake wajen makaranta
  • An ga gawawwakin tumbur a dakin matashin mai suna Daniel inda har a halin yanzu ba a tabbatar da abinda yayi ajalinsu ba
  • Dalibai 'yan uwansu sun daina ganinsu na tsawon kwana 3 a yayin da suke jarabawa, hakan yasa suka je dakinsu inda suka tarar da mummunan lamarin

Kwara - An tsinta gawar Malete Tobiloba Daniel tare da wata da ake zargin budurwarsa ce mai suna Arewa Abayomi duk daliban jami'ar jihar Kwara a dakin kwanan Daniel dake wajen makarantar, Daily Trust ta rahoto.

Mamatan dukkansu daliban aji biyu ne a jami'ar kuma suna tsaka da rubuta jarabawa ne lokacin da lamarin ya faru.

'Yan sanda
An Tsinta Gawar Ɗaliban Jami'a Masoyan Juna Tsirara a Ɗakin Kwanansu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wani dalibin KWASU ya tabbatar da cewa:

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan Daba Sun Kone Gidan 'Yan Shi'a, Kadarorin N3m Sun yi Kurmus

"Muna tsammanin masoya ne kuna mun damu lokacin da muka ga sun kwashe kwanaki uku basu zuwa jarabawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Daga nan ne wasu daga cikin abokansu suka je dakinsu dake wajen makarantar kuma suka same su tsirara a mace. Muna zargin guba suka ci."

Mai magana da yawun jami'ar KWASU, Hajiya Saeedat Aliyu, tace a hukumance bata samu labarin komai ba game da lamarin.

A daya bangaren, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Ajayi Okasanmi, ga tabbatar da aukuwar lamarin inda yace:

"Bayanin shine an tsinta gawarsu a dakinsu dake wajen makaranta kuma an sanar da 'yan sanda.
"Jami'anmu sun rufo kofar kuma an kai su asibitin koyarwa na jama'ar Ilorin domin gane abinda ya halaka su. Ana bincike kan lamarin."

Matashi Mai Shekaru 25 ya Make Matar Babansa da Tabarya, Ya Bayyana Dalilinsa

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Katsina a ranar Alhamis tace ta kama matashi mai shekaru 25 mai suna Najib Shehu wanda yayi amfani da tabarya wurin halaka matar babansa.

Kara karanta wannan

Washegarin Biki, Ango da 'Yan Biki 5 Sun Sheka Lahira, Wasu Suna Asibiti Rai a Hannun Allah

Kamar yadda rundunar 'yan sandan tace, lamarin ya faru a ranar Alhamis da ta gabata kuma a kowanne lokaci za a iya gurfanar da shi a gaban kotu.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isah, ya bayyana hakan jim kadan bayan kama Shehu a hedkwatar rundunar a Katsina. An bayyana shi tare da tabaryar da yayi amfani da ita wurin halaka matar mai shekaru 60.

Asali: Legit.ng

Online view pixel