Kungiya Ta Roki Gwamna Wike Ya Yi Watsi da Atiku, Ya Koma Bayan Obi a 2023

Kungiya Ta Roki Gwamna Wike Ya Yi Watsi da Atiku, Ya Koma Bayan Obi a 2023

  • Wata kungiya ta nemi gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya mance da Atiku da Tinubu, ya mara wa Peter Obi baya a 2023
  • Shugaban ƙungiyar, High Chief Felix Ogbegbor, ya ce Obi yana da tarihin gaskiya kuma ya fi sauran ƴan takara cancanta da kwarewa
  • A makonnin nan, gwamna Wike ya gana da dukkan yan takarar guda uku yayin da ake tunkarar zaɓen 2023

Rivers - Ƙungiyar baƙi mazauna jihar Ribas ta yi kira ga gwamnan jihar, Nyesom Wike, ya koma bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, domin ya gaji Buhari a 2023.

Punch ta rahoto cewa, ƙungiyar ta shawarci Wike ka da ya saki tsohon gwamnan Anambra (Obi) wanda ke da ƙarancin shekaru idan aka kwatanta yan takarar manyan jam'iyyu biyu.

Dan takarar LP, Peter Obi.
Kungiya Ta Roki Gwamna Wike Ya Yi Watsi da Atiku, Ya Koma Bayan Obi a 2023 Hoto: punchng
Asali: UGC

Shugaban ƙungiyar, High Chief Felix Ogbegbor, shi ne ya yi wannan kiran yayin zantawa da manema labarai a Patakwal, babban birnin jihar Ribas.

Kara karanta wannan

2023: Daga Karshe, Shekarau Ya Yanke Jam'iyyar Da Zai Koma Bayan Ganawa da Atiku da Tinubu

Ogbegbor, ya ce bai kamata Wike ya yi kuskuren goyon bayan ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar, ko na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ba, inda ya bayyana cewa ba zasu iya tabuƙa wa kasar nan komai ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa, lokacin Obi yake matsayin gwamnan Anambra ya yi abin a zo a gani kuma ya bar tarihi mai tsafta. Ya nuna cewa ɗan takarar na da Ajendar gyara Najeriya.

Ogbegbor ya kara da bayanin cewa a tsakanin masu neman kujerar shugaban ƙasa na jam'iyyun APC, PDP da LP, Peter Obi ya fita daban kuma ya fi cancanta saboda yana da gaskiya, don haka suke kira ga Wike ya mara masa baya.

Waya yafi dacewa ya karɓi Najeriya a 2023?

Shugaban ƙungiyar ya ce a halin yanzun Najeriya ba ta bukatar jagoran da ya zarce shekara 70. Ya yi ikirarin cewa Atiku da Tinubu ba zasu iya tsamo Najeriya daga kalubalen taɓarɓarewar tallalin arziki da tsaro ba.

Kara karanta wannan

Hotuna: Tinubu, Shettima, Adamu da Jiga-Jigan APC Sun Sa Labule a Abuja bayan Ganawa da Wike

Ya ce, "Ina tunanin Obi ya fi dacewa Wike ya mara wa baya, ba abinda Atiku da Tinubu zasu iya. Idan ba zasu janye ba, kamata ya yi Wike ya goyi bayan Peter Obi, bamu son tsoho, sauran sun haura shekara 70."

"Idan Wike ya goyi bayan Obi to muna bayansa ɗari bisa ɗari," In ji shi kuma ya bayyana cewa ƙungiyar da ta ƙunshi baƙi mazauna jihar daga sassan Najeriya ta kaɗa kuri'ar kwarin guiwa kan Wike.

A wani labarin kuma An Sanya Lokacin Sauya Shekar Shekarau Zuwa PDP, Atiku Zai Fara Zawarcin Wasu Yan Siyasan Kano

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, zai koma jam'iyyar PDP a hukumance yau Litinin.

Wata majiya ta ce manyan kusoshin PDP sun sa labule da Sanatan jiya Lahadi domin tsara komai game da lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262