Bayan Doguwar Tattaunawa, Kungiyar ASUU Ta Sake Kara Wa’adin Yajin Aikin da Take Ciki
- Kungiyar malaman jami'a a Najeriya ta bayyana sake kara wa'adin yajin da ta tsunduma tun watan Fabrairu
- Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyar malaman jami'a ASUU kan wasu matsaloli
- Daliban jami'a a Najeriya na ci gaba da kama sana'a, domin karatun jami'o'in gwamnati na kokarin fin karfinsu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jaridar Punch ta ce ta samo cewa, bayan doguwar tattaunawa mai dauke da maganganu da hange, kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ta yanke shawarar tsawaita wa'adin yajin aikin da take ciki.
Kungiyar ta dauki wannan matakin ne bayan zaman majalisar zartarwar na kasa da aka yi a hedikwatar kungiyar da ke Jami’ar Abuja da sanyin safiyar yau Litinin 29 ga watan Agusta.
Kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki tun ranar 14 ga watan Fabrairu, ya zuwa yanzu ta ashafe kwanaki sama da 195 a cikin yajin, rahoton Leadership.
Mashahurin Mai Kudin Duniya, Elon Musk, Yace Mahaifiyarsa a Gareji Take Kwana Idan ta Kai Masa Ziyara
A bangaren gwamnati, mai magana da yawun ma'aikatar ilimi, Ben Goong ya bayyana cewa, gwmanati ta yi iya kokarinta waje tabbatar da an kawo karshen yajin aikin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce:
“Batun mataki na gaba, tuni gwamnati ta kaddamar da kwamitin daidaita tsarin IPPIS, UTAS, da UP3.
"Wannan zai tabbatar da cewa gwamnati za ta ke biyan albashi ta hanya daya kacal kuma hakan zai daidaita duk wata danbarwa ta fasaha.
“Idan ka bijiro da bukatu kuma aka biya 80% cikin 100%, babu bukatar a jan yajin aiki kuma.
"Bai dace a ci gaba da yajin aikin ba ganin yadda gwamnati ta kokarta wajen biyan mafi yawan bukatun."
A Ci Gaba da Yi: Dalibin Jami’a Ya Kama Sana’a, Ya Ce ASUU Su Tabbata Suna Yaji Kawai
A wani labarin, Abdulhadi Dankama ya samu shiga sashen ilmin lissafi a jami'ar Bayero ta jihar Kano domin yin digirinsa na farko.
Ya kamata Dankama ya kammala digirinsa a yanzu idan da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta fara ba kan rashin jituwa da gwamnatin tarayya bata shafe shi ba.
Za ku yi tunanin Dankama wanda a yanzu yana aji 3 zai kosa ya koma makaranta domin ya gaggauta kammala karatunsa.
Asali: Legit.ng