Kano: 'Yan Daba Sun Kone Gidan 'Yan Shi'a, Kadarorin N3m Sun yi Kurmus
- Wasu bata-gari da ba a san ko su waye ba sun kone gidan da mambobin kungiyar shi'a ke amfani da wurin tarukansu
- Ba taro kadai ba, shugaban cibiyar, Dr Sulaiman Gambo yace suna karatu kuma suna ajiyar kayayyakinsu a gidan dake Dorayi Babba
- Ya bayyana yadda aka haura katangar gidan tare da babbaka shi da wasu kadarori da zasu kai na N3 miliyan
Kano - Wasu 'yan daba sun kone gidan da mambobin Shi'a ke amfani da shi wurin taro, karatu da ma'ajiyar kayayyaki a Dorayi babba dake karamar hukumar Gwale ta jihar Kano.
Daily Trust ta rahoto cewa, shugaban cibiyar, Dr Sulaiman Gambo ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yace 'yan daban sun tsallako ta katanga kuma suka kone ginin da ma'ajiyar kayayyakin da suka kai darajar N3 miliyan.
"Mun kai rahoto har ofishin 'yan sandan Dorayi babba kuma DPO da kanshi ya zo da wasu jami'ai don duba lamarin. Mun aike da korafin barazana ga rayuwa da kadarori ga kwamishinan 'yan sanda," yace.
Gambo yace a ranar 2 ga watan Augusta da ya gabata an kai wa mambobinsu farmaki yayin da suke wani taro inda aka raunata biyar tare da kone motarsu.
Ya yi kira ga hukumomin da lamarin ya shafa da su zakulo miyagun dake wannan mugun aikin wadanda suka sha alwashin hana 'yan Shi'a damarsu ta bauta.
A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Kiyawa, yace bai riga da ya samu rahoto ba amma za a ji shi idan ya kammala bincike.
Kiyawa yayi kira ga mazauna yankin da su rungumi zaman lafiya da mutunta addinan juna.
Matashi Mai Shekaru 25 ya Make Matar Babansa da Tabarya, Ya Bayyana Dalilinsa
A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Katsina a ranar Alhamis tace ta kama matashi mai shekaru 25 mai suna Najib Shehu wanda yayi amfani da tabarya wurin halaka matar babansa.
Kamar yadda rundunar 'yan sandan tace, lamarin ya faru a ranar Alhamis da ta gabata kuma a kowanne lokaci za a iya gurfanar da shi a gaban kotu.
Kakakin rundunar, SP Gambo Isah, ya bayyana hakan jim kadan bayan kama Shehu a hedkwatar rundunar a Katsina. An bayyana shi tare da tabaryar da yayi amfani da ita wurin halaka matar mai shekaru 60.
Asali: Legit.ng