Sokoto: An Kama Dagajin Kauye Kan Dillancin Wiwi Da Miyagun Kwayoyi
- Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta kama mai gari a Sokoto kan dillancin miyagun kwayoyi
- Femi Babafemi, Kakakin Rundunar NDLEA ta ce wannan shine karo na biyu da ake kama Alhaji Umaru Mohamed kan safarar miyagun kwayoyin
- Mai magana da yawun na NDLEA ya ce an samu kwayoyi kamar tabar wiwi da diazepam a gidan mai garin kuma za a gurfanar da shi a kotu
Jihar Sokoto - Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa NDLEA ta ce ta kama dagajin kauyen Ruga, a karamar hukumar Shagari kan laifin sayar da muggan kwayoyi, Daily Trust ta rahoto.
Kakakin rundunar ta NDLEA ya ce an kama Alhaji Umaru Mohammed wanda aka fi sani da Danbala ne a ranar 22 ga watan Agustan 2022
Ba wannan ne karon farko da aka kama shi da muggan kwayoyi ba
Kafin kama shi a baya-bayan nan inda aka gano tabar wiwi mai nauyin kilogram 436.381 da diazepam mai nauyin kilogram 1 a gidansa, a baya an taba kai samame gidansa an kama wasu kwayoyin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwayoyin da aka kama a samamen farkon a ranar 20 ga watan Yulin shekarar 2022 sun hada da kilogram 11.5 na tabar wiwi, kilogram 2.259 na exol5 da kuma kilogram 500 na diazepam.
Za a gurfanar da shi a gaban kotu da zarar an kammala bincike a cewar mai magana da yawun na NDLEA.
Shugaban hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyin na kasa, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya) ya yaba wa jami'an rundunar bisa nasarar da suka yi na kama wadanda ake zargin da kuma kwato kwayoyin.
Dakaci karin bayani ....
Asali: Legit.ng