Da Duminsa: Tubabben Sarkin Zamfara Ya Kwanta Dama a Dubai
- Tsohon Sarkin Zurmi a jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Atiku, ya riga mu gidan gaskiya a wani asibiti dake Dubai
- Sarkin da Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya tubewa rawani a shekarar da ta gabata, ya rasu sakamakon jinyar da yayi fama da ita
- Kamar yadda iyalansa suka bayyana, har yanzu ba a dawo da gawarsa gida Najeriya ba domin masa jana'iza
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Zamfara - Korarren Sarkin Zurmi na jihar Zamfara, Abubakar Atiku, ya rasu a Dubai, babban birni a Haddadiyar Daular Larabawa.
Atiku ya rasu a wani asibiti mai zaman kansa dake Abu Dhabi bayan fama da gajeriyar rashin lafiya da yayi da ita.
Wani daga cikin iyalansa, Sani Zurmi, ya sanarwa da The Punch cewa ba a riga da ana dawo da gawar tsohon basaraken ba Najeriya domin jana'iza.
“Har yanzu gawarsa tana Dubai saboda rashin jirgin da za a dawo da shi gida domin jana'iza," Zurmi yace.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Punch ta rahoto cewa, an tube mamacin daga kujerarsa tare da Sarkin Dansadau, Husaini Umar a ranar 27 ga watan Afirilun 2021 kan zarginsu da taimakawa ta'addanci.
Hotuna: Yadda aka yi bikin naɗin sarautar riƙaƙen ɗan ta'addan da FG ke nema ido rufe
A wani labari na daban, an yi wa rikakken dan ta'adda Ado Aleru, nadin sarautar Sarkin Fulani a masarautar 'Yandoton daji dake jihar Zamfara.
'Yandoton daji tana daya daga cikin sabbin masarautu biyun da gwamnatin jihar Zamfara ta kirkiro a watan Mayun da ya gabata.
An kirkiro ta ne daga masarautar Tsafe. Sabon sarkin Yandoton Daji shine Aliyu Marafa.
Hukuncin bai wa shugaban 'yan bindigan sarauta ya biyo baya ne sakamakon kokarin da yayi na tabbatar da zaman lafiya tare da jagorantar yarjejeniya tsakanin masarautar da 'yan ta'addan da suka addabi karamar hukumar Tsafe.
Asali: Legit.ng