Babu Kudi A Harkar Fim: Jarumin Fim Ya Nemi EFCC Da NDLEA Su Binciki Jarumai Maza Da Ke Siyan Manyan Gidaje

Babu Kudi A Harkar Fim: Jarumin Fim Ya Nemi EFCC Da NDLEA Su Binciki Jarumai Maza Da Ke Siyan Manyan Gidaje

  • Jarumin fina-finan Nollywood ya kalubalanci EFCC da NDLEA da su fara binciken jaruman fim maza da ke gina manyan gidaje
  • Uche Maduagwu ya ce ko kadan babu kudi a cikin harkar fim da har za su iya mallakar manyan kadarori
  • A cewarsa jarumai irin su Jim Iyke da wasu yan kadan ne za su iya mallakar gidajen saboda tarin talullukan da suke samu daga kamfanoni

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Jarumin fina-finan kudancin kasar, Uche Maduagwu, ya bukaci hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) da hukumar yaki da hana fatcin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) da su binciki jarumai maza da ke siyan manyan gidaje.

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Instagram, jarumin ya ce ya kamata a binciki yan fim da ke kasa da shekaru 38 wadanda ke siyan kadarori.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: ASUU ta shawarci Buhari kan yadda za a kawo karshen yajin aiki

Uche Maduagwu
Babu Kudi A Harkar Fim: Jarumin Fim Ya Nemi EFCC Da NDLEA Su Binciki Jarumai Maza Da Ke Siyan Manyan Gidaje Hoto: uchemaduagwu
Asali: Instagram

A cewarsa, babu kudi ko kadan a cikin masana’antar shirya fina-finan.

Jarumin ya kuma bayyana cewa mutum kamar Jim Iyke da wasu yan tsirarun tsoffin jarumai ne kadai za su iya siyan wadannan manyan gidajen domin kowa ya san hanyoyin samun kudinsu wajen yin talulluka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalli wallafar tasa a kasa:

Jama’a sun yi martani

stephen.uzochukwu ta yi martani:

“Ta iya yiwuwa gaskiya ne.”

eberechi700 ta ce:

“Ba za ka iya yaudarata ba

andreasilas22 ya ce:

“Kishi ne.”

iam__ovwis ta ce:

“Katon wawa ne kai.”

Kudi Kare Magana: Bidiyon Katafaren Gida Da Wani Matashi Ya Kera Cikin Watanni 4

A wani labarin, wani matashi dan Najeriya ya je shafin soshiyal midiya don murnar kammala ginin gidansa na biyu a cikin watanni 4.

Matashin wanda ke amfani da shafin @kelvinwhite12 a TikTok ya wallafa wani bidiyo da ke dauke da yadda aka fara aikin gidan da kammala shi.

Kara karanta wannan

Wata 6: Duk da aikin Hisbah, rahoto ya fadi kudin da 'yan Najeriya suka kashe a shan giya

Shafin farko ya nuna lokacin da aka fara ginshikin gidan da masu aikin gini suna ta aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng