'Yan Sanda Sun Saki Sabon Bayani Kan Mutanen Da Suka Kashe Deborah a Sakkwato

'Yan Sanda Sun Saki Sabon Bayani Kan Mutanen Da Suka Kashe Deborah a Sakkwato

  • Rundunar yan sandan jihar Sakkwato ta fitar da sabon bayani kan Kes ɗin kisan Deborah Samuel, ɗalibar da ta yi batanci ga Annabi SAW
  • Mai magana da yawun yan sanda, Sanusi Abubakar, ya ce sun baza komar su ta ko ina domin kama asalin masakasan Deborah
  • A cewarsa, mutanen da ke hannu sun taimaka wajen ta da rikicin amma ba su ne waɗan da ake zargi da kisan ba

Sokoto - Rundunar yan sanda reshen jihar Sakkwato ta ce har yanzu dakarunta na cigaba da neman waɗan da ake zargi da kisan ɗalibai kwalejin tuna wa da Shehu Shagari, Deborah Samuel.

Wasu fusattatun mutane da ake tsammanin ɗalibai ne sun kashe Deborah a watan Mayu, 2022 kan zargin ta da yin kalaman ɓatanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Yi Wa Ayarin Sojoji Kwantan Bauna, An Yi Kazamar Musayar Wuta, Da Yawa Sun Mutu

Marigayya Deborah Samuel.
'Yan Sanda Sun Saki Sabon Bayani Kan Mutanen Da Suka Kashe Deborah a Sakkwato Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kakakin rundunar yan sandan, DSP Sanusi Abubakar, wanda ya zanta da Punch ranar Lahadi kan Kes ɗin ya ce waɗan da suka shiga hannu ba su ne asalin makasan ɗalibar ba, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Abubakar ya ƙara da cewa mutanen na da hannu ne a tayar da bore kawai amma ba sune asalin waɗan da ake zargin da kisan ba kuma har yanzun suna tsare kamar yadda Kotu ta umarta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ina aka kwana wajen kama waɗan da ake zargin?

Kakakin yan sandan ya bayyana cewa waɗan da ake zargi a sahun farko kan kisan har yanzun ba su shiga hannu ba, amma jami'ai na cigaba da kokarin gano su da cafke su.

A jawabinsa, mai magana da yawun yan sandan Sakkwato ya ce:

"Waɗan da muka kama duk da ba su ake zargi da kisan ba, sun taka rawa wajen ta da bore kuma mun gurfanar da su a Kotu, inda Alƙali ya ba da umarnin a garkame su."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Harbe Babban Jami'in Ɗan Sanda Har Lahira

"Game da makasan kuma mun yaɗa Hotunan su a kafafen sada zumunta kuma mun girke jami'an tattara bayanan sirri a dukkan sassan jiha, har yanzu idon mu na kan su kuma muna da yakinin kama su ko ina suka ɓuya."

Abubakar ya tabbatar da cewa hukumar ƴan sanda ba zata rangwanta wa kowa game da lamarin ba, inda ya kara da cewa kwamishinan ƴan sanda, Muhammed Gumel, zai tabbatar da an yi adalci.

A wani labarin kuma Rundunar Sojin Najeriya Ta Yanke Wa Sojojin Da Suka Kashe Sheikh Goni Hukunci

Rundunar sojin Majeriya ta kori sojoji biyu da ake zargi da kisan Sheikh Goni Aisami Gashuwa a jihar Yobe.

Kwamitin da rundunar soji ta kafa domin gudanar da bincike kan lamarin ya kammala aikinsa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel