An Dakatar Da Wasu Yan Sanda Mata 2 Saboda Bidiyon 'Rashin Da'a' Da Suka Wallafa A TikTok

An Dakatar Da Wasu Yan Sanda Mata 2 Saboda Bidiyon 'Rashin Da'a' Da Suka Wallafa A TikTok

  • Rundunar yan sandan Najeriya ta dakatar da wasu jami'anta mata biyu kan zargin saba dokokin amfani da soshiya midiya
  • Kakakin rundunar yan sanda, Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a 26 ga watan Agusta
  • Sanarwar ta ce irin shigar da jami'an suka yi a bidiyon ya saba tarbiyya da koyarwan aikin yan sanda don haka dakatarwar da aka musu ya fara aiki nan take

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT Abuja - Rundunar yan sandan Najeriya ta dakatar da wasu jami'anta biyu da aka gani a wani bidiyon Tiktok da ya bazu saboda saba dokar amfani da soshiyal midiya ta rundunar.

An dakatar da Obaze Blessing da Obaze Emmanuella Uju ne nan take saboda wallafa bidiyon da ya saba dokokin aikin dan sandan Najeriya nan take, a cewar kakakin yan sanda, Olumuyiwa Adejobi cikin sanarwar da ya fitar ranar Juma'a 26 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

An Kama Mutumin Da Ya Lakaɗa Wa Jami'in Ɗan Sanda Duka A Legas

Yan sanda da aka dakatar
An Dakatar Da Wasu Yan Sanda Mata 2 Saboda Bidiyon Da Suka Wallafa A TikTok. Hoto: @PremiumTimesNg.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rundunar ta ce abin da jami'an suka aikata ya saba tanadin dokar Police Act, 2020, da dokokin daukan aiki/karin girma/ladabtarwa na yan sandan sirri wato (SPY) 2013 na sufeta janar na yan sanda. Dokar yan sandan sirri wadanda mukaminsu ya wuce mataimakin sufritanda ta hana su saka unifom.

Dakatattun yan sandan - Obaze Blessing mai lamba ta SPY 5709, da Obaze Emmanuella Uju mai lamba ta SPY 5708, sun kawata kansa da kayan yan sanda a bidiyon wanda ya saba wa dokar SPY.

Daya daga cikinsu ta kawata kanta da mukamin sufritanda na yan sanda wanda ya saba wa doka.

Baya ga haka, sun nuna kansu a bidiyon da bazu da wasu bidiyoyin a yanayin rashin tarbiya da kwarewa, wanda ya saba wa dokar amfani da soshiyal midiya na yan sanda tare da nuna kudin da aka samu ta haramtacciyar hanya da tarbiya marasa kyau, wanda mutane da dama suka yi tir da shi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Sanda Sun Rufe Sabuwar Ofishin NNPP A Borno, An Kuma Kama Shugaban Jam'iyyar

An kama sojan gona da kayan hukumar FRSC dauke da katin shaidar aikin soja a Kano

A wani rahoton, jami'an hukumar kiyaye hadura na kasa (FRSC) da hukumar yan sanda sun kama wani mutum mai suna Injiya Gude Ude a jihar Kano da kayan jami'an hukumar kiyaye hadura FRSC kuma dauke da katin shaidar aikin sojan a garin Kano.

Sanarwan da hukumar FRSC ta bayar mai dauke ta sa hannun mukadashin Secta Kwamanda, Ahmed T. Mohammed ta cean kama Ude ne a ranar Alhamis, 4 ga watan Janairun 2018 a titin Kaduna - Kano a yayin da rundunar ke gudanar da wata kewaye na musamman da akayi wa take da "Operation Zero"

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164