Rahoto Ya Nuna Najeriya Ta Samar da Wutar Lantarki Mafi Yawa a Mulkin Buhari

Rahoto Ya Nuna Najeriya Ta Samar da Wutar Lantarki Mafi Yawa a Mulkin Buhari

  • Sabon rahoto ya bayyana yawan samuwar wutar lantarki a karkashin mulkin shugabannin Najeriya hudu tun 1999
  • Abun mamaki shine yadda mulkin shugaba Buhari ya zo na farko a fannin samuwar wutar fiye da Obasanjo, Yar'Adua da Jonathan
  • Wannan na zuwa ne lokacin da kamfanonin samar da wutar lantarki a Najeriya ke korafin cewa shan wutar lantarkin 'yan Najeriya tayi yawa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Sabon rahoto daga StatiSense ya bayyana cewa Najeriya ta samar da wutar lantarki mafi yawa a karkashin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari fiye da sauran gwamnatocin farar hula da suka gabata.

Kamar yadda bayanan StatiSense suka nuna, karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, an samu karin wutar lantarki a Najeriya har 8 terawatt a kowacce sa'a daya.

Shugaban kasa
Rahoto Ya Nuna Najeriya Ta Samar da Wutar Lantarki Mafi Yawa a Mulkin Buhari. Hoto daga Presidency
Asali: Facebook

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a daya bangaren yayin mulkinsa ya kara 7Twh na wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Sunayen Jihohi 7 da Kananan Hukumominsu da 'Yan Ta'adda ke Barazanar Hana Zaben 2023

Marigayi Shugaba Umaru Musa Yar'Adua ya kara 3Twh sai tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kara 6Twh a yayin da yake mulkinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan Najeriya sun yi martani

Sunayen Jihohi 7 da Kananan Hukumominsu da 'Yan Ta'adda ke Barazanar Hana Zaben 2023

A wani labari na daban, al'amarin rashin tsaro a Najeriya ya dauka fuskar ban tsoro ta yadda sama da kananan hukumomi 40 a sassa daban-daban na kasar nan ke karkasin ikon 'yan bindiga, 'yan ta'adda da 'yan bindigan da ba a sani ba.

Wuraren dake karkashin ikon 'yan ta'addan suna cikin jihohin Kaduna, Zamfara, Niger, Katsina, Sokoto, Abia da Imo.

Wannan lamari babu shakka babbar barazana ce ga zaben 2023 ballantana tsaron ma'aikatan zabe da masu kada kuri'u a inda 'yan ta'adda ke mulka ba abu bane mai tabbas.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Dalilin ganawar Wike da Atiku, Tinubu, Peter Obi da Obasanjo a Landan ya fito

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng