An Zakulo Gawarwakin Mutane Biyu da Suka Mutu a Ginin da Ta Ruguje a Abuja
- Ana ci gaba da bincike kan ginin da ya ruguje a babban birnin tarayya Abuja, an ceto wasu mutane biyar
- Rahotanni sun ce, mutum biyu sun mutu, kuma daya daga cikinsu mai gadin ginin ne da ke aiki a cikinsa
- Wani gini ya ruguje a Abuja, lamarin da ya tada hankalin jama'a tun sanyin safiyar Juma'a 26 ga watan Agusta
FCT, Abuja - Rahoton da muke samu daga jaridar TheCable ya ce, mutane biyu sun mutu bayan da suka makale a wani bene mai hawa biyu da ya ruguje a Kubwa da ke birnin tarayya Abuja.
Babban hadimi na musamman ga ministan babban birnintarayya, Ikharo Attah ne ya tabbatar da hakan a yau Juma'a 26 ga watan Agusta.
A cewar makwabtan, wani dattijo da ke gadi a benen ne ya rasu da kuma wani abokinsa da suke tare a lokacin.
Da sanyin safiyar yau Juma'a ne aka tashi da mummunan labarin yadda ginin bene mai hawa biyu da ake ginawa ya rushe a Abuja.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Rahotanni a baya sun ce, an yi nasarar ceto ma'aikata biyar, wanda suka mutun kuwa tun farko sun makale ne a karkashin ginin, rahoton ThisDay ma haka yace.
Wani mazaunanin yankin mai suna Emmanuel Omeke ya shaida wa manema labarai cewa ginin a baya kantin siyayya ne kafin daga bisani aka mayar dashi gidan zama.
Ya ce akwai yiwuwar karin wasu gine-gine a jikin benen ya turasa shi zuwa rugujewa.
Jami’an hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) da na Civil Defence sun hallara jim kadan bayan rushewar ginin.
Katon Bene ya Rushe, Ya Murkushe Ma'aikata da Yawa a Abuja
A tun farko, wani bene mai hawa biyu da ake tsaka da gininsa ya rikito a yankin Kubwa dake Abuja, lamarin da ya kawo dannewar ma'aikata a cikin ginin.
Jami'an Hukumar Kula da Taimakon Gaggawa, NEMA, suna kokarin ceto jama'ar da ginin ya murkushe a yayin da Daily Trust ta ziyarci wurin.
Har yanzu babu tabbacin yawan wadanda lamarin ya shafa, amma wani mazaunin yankin yace wadanda suka samu rauni an kwashesu tare da mika su asibiti.
Asali: Legit.ng