Wata Mata Ta Sayar Da Jaririn Da Ta Haifa Mako Uku N600,000 a Ogun

Wata Mata Ta Sayar Da Jaririn Da Ta Haifa Mako Uku N600,000 a Ogun

  • Dakarun yan sanda sun kama wata matashiya yar shekara 23 da ta siyar da jaririn da ta haifa kafin fatiha a jihar Ogun
  • Matar, wacce ta amsa laifinta ta ce wata ƙawarta ce ta kaita wurin wanda ya siya kan kuɗi N600,000 suka raba kuɗin
  • Hukumar yan sanda tace tun farko Saurayin matar da suka haifi jaririn ne ya kai rahoton abinda ya faru

Ogun - Jami'an hukumar yan sanda reshen jihar Ogun sun kama wata mata ƴar shekara 23, Mary Olatayo, bisa zargin ta sayar da jariri ɗan mako uku kan kuɗi N600,000.

Daily Trust ra rahoto cewa wacce ake zargin ta shiga hannu ne bayan mahaifin jaririn ya shigar da ƙorafi a Ofishin yan sanda dake Mowe, ƙaramar hukumar Obafemi-Owode, jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Iyayen zaman: Uba ya rufe shagon 'yarsa saboda ta ki amince a tafi da ira Italiya yawon karuwanci

Matar da ta siyar da ɗanta.
Wata Mata Ta Sayar Da Jaririn Da Ta Haifa Mako Uku N600,000 a Ogun Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Kakakin hukumar yan sanda, Abimbola Oyeyemi, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abeokuta ranar Alhamis.

Ya ce Mahaifin jaririn ya shaida wa ƴan sanda cewa ya jima suna soyayya da wacce ake zargin kuma Allah ya azurtata da ɗaukar cikinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar mai magana da yawun yan sandan, Mutumin ya ce bayan ta samu ciki ya kama mata gidan haya inda ta zauna ta raini cikin har Allah ya sauke ta, aka samu ɗa namiji.

"Mahaifin ya ƙara da ƙorafin cewa ya nemi matar ya rasa daga gidan mako uku da haihuwar jaririn, sai daga baya ya ganta a Hotel inda ta je shaƙatawa da wani mutumin daban."

"Duk yadda aka juya ta faɗi inda ta kai jaririn amma matar nan ta ƙekashe ƙasa," inji Kakakin yan sandan, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Harbe Hadimin Jigon APC Har Lahira a Wurin Shagalin Karin Shekara

Matakin da hukumar yan sanda ta ɗauka?

Bayan karɓan wannan rahoto, Shugaban Caji Ofis ɗin, SP Folake Afeniforo, ya haɗa tawaga suka dira wurin suka kamo wacce ake zargi zuwa Ofishin.

"Yayin bincike, Mary Olatayo, ta amsa cewa ta cefanar da jaririn ga wani mutumi a jihar Anambra kan kuɗi N600,000. Ta yi bayanin cewa ƙawarta Chioma Esther Ogbonna ce ta kaita wurin mai sayen kuma tare suka raba kuɗin."

Oyeyemi ya ce bayanan wacce ake zargin ne ya yi sanadin cafke ƙawarta Chioma Esther Ogbonna. Da aka tsananta bincike an gano cewa matashiyar yar hannu ce, ganin jaririn zai rage mata kasuwa ya sa ta nemi hanyar rabuwa da shi.

A wani labarin kuma Fitaccen Jarumin Fina-Finai a Najeriya Ya Fice APC, Ya Koma Bayan Wanda Yake So Ya Gaji Buhari a 2023

Fitaccen Jarumin fina-finai da ya watsar da APC saboda takara Musulmi da Musulmi ya koma jam'iyyar LP.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Yan Uwan Ɗan takarar Gwamna a Jihar Shugaban Ƙasa

Kenneth Okonkwo, ya nuna jin daɗinsa ganin yadda aka girmama shi a LP yayin tabbatar da sauya shekarsa a hukumance a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262