A Gaggauta Hukuntashi Kada Dalibai Su Harzuka: Martanin Yan Yobe Kan Sojan Da Ya Kashe Sheikh Aisami

A Gaggauta Hukuntashi Kada Dalibai Su Harzuka: Martanin Yan Yobe Kan Sojan Da Ya Kashe Sheikh Aisami

  • Sojan da ya kashe babban Malami a jihar Yobe ya bayyana abinda Sheikh Goni Aisamu ya fada masa yayinda ya daga bindiga zai harbesa
  • Hukumar yan sanda ta bayyana sakamakon bincikenta kan Sojojin da akewa zargin kisan Sheihk Goni Aisami
  • An yi jana'izar Shehin Malamin mazauni jihar Yobe ranar Asabar kuma dubban mutane sun hallara

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Damaturu - Lance Kofur John Gabriel ya bayyana yadda ya yaudari Sheik Goni Aisami-Gashua, kafin harbinsa da bindiga har lahira a kan titin Gashua- Jaja Maji.

Yayinda jawabi lokacin da yan sanda suka gabatar da shi gaban yan jarida ranar Laraba, Kofur John ya ce babban Malamin ya yi masa tambayoyi biyu yayinda yake kokarin kashe shi, rahoton DailyTrust.

Yace:

"Yayinda muka kusa Jaji-Maji kuma tagogin motar na sauke, sai na fada masa ina jin kara karkashin motarsa, sai yace shima yana ganin akwai wani abu."

Kara karanta wannan

Maganata Ta Karshe Da Mijina Yayinda Ya Hau Hanya, Uwargidar Sheikh Goni Aisami

"Sai ya faka motar. Yayinda ya tsaya a gefen hanya ya fita daga motar, sai na bi sa. Bayan ya gama dubawa bai ga komai ba."
"Ni kuma tuni na fito da bindiga da harsashi lokacin da yake duba motar. Da bai ga komai ba, sai na nuna masa bindiga, sai ya tambayeni, 'Me na maka?" Ni kuma na bashi amsa, babu abinda kayi min."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Sai ya sake tambaya na, 'Kana son ka kashe ni ne?' Sai na nace masa Bana son kashe ka' Sai yayi shiru. Sai na harba bindiga don tsoratar da shi ina tunanin zai gudu. Amma bai gudu ba, sai ya shiga cikin motar, sai na bindigeshi."

Gideon
Abinda Sheikh Goni Aisami Ya Fada Min Yayinda Na Daga Bindiga Zan Harbesa: Barawon Soja Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Legit ta yi hira da wani mazaunin Damaturu, Karagama Al-Mahmoud, wanda ya bayyana halin da al'ummar garin suka shiga sakamakon kisan babban malamin.

Kara karanta wannan

Mu ba butulu bane: Tinubu ne zan gaji Buhari a 2023, Insha Allahu, Masari ya bayyana dalilai

Ya bayyana cewa al'ummar garin na jimami matuka bisa abinda ya faru kuma suna sauraron abinda gwamnati za ta yiwa makasan.

A cewarsa, kawo yanzu dai babu wani tashin hankali amma yana kira ga gwamnati ta gaggauta yin hukunci kan makashin gudun kada mutane da dalibansa su harzuka idan ba'a dau mataki ba.

Shahrarren Lauya kuma masani harkokin tsaro, Bulama Audu Bukarti, wanda shima dan jihar Yobe ne ya bayyana cewa tun da Sojan ya amince ya aikata laifin, kada ayi jinkiri wajen hukuntashi.

Yace:

"Gaggauta hukuntashi zai kwantar da hankalin iyalai da daliban Sheikh kuma ya zama darashi da masu kayan sarki barayi."

Kalli bidiyon:

Legit ta tattaro muku martanin Jama'a kan wannan maganar da yayi

Zenret John yace:

"Allah ya tsine maka albarka. Gaskiya adaina daukan marasa hankali a aikin soja."

Maman Muhammad Aabideen tace:

"Allahu Akbar kaga me cikakken Imani se ya nuna masa babu me daukar ran wani sai Allah saidai kazama sila Allah yasa katashi cikin amintattun ubangiji."

Kara karanta wannan

'Ba Zamu Zuba Ido Ba' Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki Kan Batun Kisan Sheikh Goni Aisami a Yobe

Kai Kuma Kofur Allah yasadaka da mafificin bakincikin duniya da lahira banason kayi mutuwar far daya nafison ka mutu bayan kagama Shan wahalar duniya

Anna John Barde Tace:

"Yanzu babu yarda ko kadan. mutum Soja. Allah yayi mana rahama. Allah ya jikansa

Haruna Rashid Zakari yace:

"Mudage dayiwa kasarmu Addua
ALLah Ubangiji Ya Kawo Mana Karshen Wannan Museeba Ta Rashin Tsaro A Nigeria Alfarmar Sayyadinah Muhammadu Rasulillahi SAW."

Amina Ali Captain tace:

"Allah ya wulaqanta ka azzalumi ya dawwama ka a wuta mafi tsananin azaba Allah yjknk malam yasa can tafi nan shiyasa ko ya nake da mutum idan zanyi long journey ba,a shigarmin mota wasu suna ganin kmr girman kai ne Kuma irin wdnnn mtslln sune abin gudu katemaki mutum shi Kuma ya ga bayan ka wannan abin tausayi zai Dade bai bar zcy Mai Imani ba."

Ishaku Yohannah yace:

"Ni ban san ganin wannan labarin, wannan abin takaici ne. Ka dauki ran mutum haka kawai? Wannan mutum bakin mugu ne."

Kara karanta wannan

A Rabu Da Wike, Yayi Duk Abinda Ya Ga Dama: Gwamna Sule Lamido

Wilson Barnabas yace:

"Wane rashin imani ne haka? wai daga taimako sai kisa? Allah ya jikan mallam, shi kuma Allah yasa ayi masa hukunci dai dai da laifinsa."

Elisha Joshua yace:

"Hukuncin kisa kadai ya cancanta a yiwa. Domin babu wata laifi da mallamin yayi Masa, sabo dahaka kisa kawai."

Mercy Lonsi tace:

"Hunkuci kuwa ya Zama dole, daga taimako don rashin tsoron Allah sai ka kashe mutum da bakataba haduwa da shi ba balle a ce yayi maka wani laifi. Allah ya sa a maka hukunci daidai da muguntarka."

زكية محمد tace:

Allah Sarki Abin tausayi Wai Me nayi maka? Allah jikanka Mallam,, Annabi ya Karbi bakoncinka.
Shi Kuma azzalumin Allah sa Suma shegun Suyi gaggawan Zartar Masa da hukunci

Da Musulmai Suka Kashe Fasto, da Batun Ya Canza - Bala Lau Ya Dauki Zafi

Shugaban kungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi karin bayani game da kisan shehin malami, Sheikh Goni Aisami da aka yi a jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Fusata, Ya Bada Umurnin Abin Da Za A Yi Wa Sojan Da Ya Kashe Sheikh Goni Aisami

Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi magana da BBC Hausa a ranar Laraba, 24 ga watan Agustan 2022, yace kisan malamin rashi ne ga Duniyar Musulmai.

A tattaunawar da aka yi da shi, Bala Lau ya sha alwashin cewa ba za su yi yarda da wannan ta’addanci ba, yace ba za su yi shiru maganar ta mutu ba.

Daily Trust ta bi hirar da aka yi, tace shugaban kungiyar ta JIBWIS ya bukaci a bi diddikin abin da ya jawo aka hallaka wannan mutumi kan hanya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel