Bidiyon Mutumin da Ya Ba Dan Najeriya ATM Dinsa Ya Ce Kudin da Yake So Ya Ba da Mamaki
- Wani mutumin kirki ya matukar ba da mamaki yayin da ya dauki katinsa na ATM ya ba mabaraci ya cire kudi
- Wannan lamari dai ya faru ne a kasar Faransa, inda mutumin ya mika katinsa ya ce wa mabaracin ya cire kudin da ya masa
- Bayan ya cire adadin kudin da yake so, sai mabaracin ya zaro ainihin katin shaidansa kana ya hau kekensa ya fece
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Wani mutumin kirkin da ya fice wajen taimakon talakawa a kasar Faransa ya bayyana gamuwarsa da wani mabaraci dan Najeriya a gefen na'urar ciran kudi ta ATM.
Kamar dai yadda ya saba, ya fara daukar bidiyo yayin da yake tunkarar wurin da na'urar ta ATM take, sai ga wani dan Najeriya mabaraci da ke kusa cikin wani irin yanayi.
A faifan bidiyon da ya yada a TikTok, mutumin ya ba dan Najeriyan katinsa na ATM, sanna ya nemi ya cire iya adadin da yake so na kudi.
Mabaracin na Najeriya ya yi wasa da sauri kan mutumin kirki
Dan Najeriyan ya danna wani adadin kudi da ya ba mai ATM din mamaki kawai don ya tabbatar a akwai kudi a asusun mutumin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, mutumin bai hana shi ko nuna damuwa ba, haka yana kallon dan Najeriyan nan ya zare kudin da ya yi masa.
Dan Najeriyan da ya ce yana nan a Faransa tun a 2019, ya godewa mutumin, kuma abin mamaki ya garzaya ga kekensa ya tuka ya wuce.
Kalli bidiyon:
Martanin 'yan Najeriya
Jane ya ce:
"Ni dan Najeriya ne, kin yin magana da ya yi da kuma nuna sana'ar aike ne bai min dadi ba."
AngelEyes ya ce:
"Watakila aikinsa bai biya da yawa kuma ana yana da nauyin iyali a aknsa, hakan ba daidai bane amma Allah zai sanya albarka a gareka."
Andrea Small ya ce:
"Ba komai, a dake yake ko yana da hali, kai dai ka yi aikin alheri dan uwa, ka bar shi kawai."
ciprian_1318 ya ce:
"Kada da damu..watakila yana bukatar wadacan kudaden.. wata kila aikinsa ne bai samu ya wadace shi."
Mutumin da Ya Kirkiri Na’urar Sarrafa Toroso Ya Yi Bayani, Yana Neman Hannun Jari
A wani labarin, wani farfesan kasar Koriya ta Kudu masi suna Cho Jae-weon ya ba da mamaki yayin da ya kirkiri wata na'urar sarrafa toroso.
A halin yanzu, farfesan toroso ya ce yana fuskantar kalubalen gaske kasancewar gwamnati ta cire masa tallafi a fasahar tasa mai suna BeeVi, wacce ke sauya toroso zuwa makamashi daga nan kuma zuwa kudin intanet.
Duk wanda ya yi amfani da wannan nau'in bandaki na juya toroso da farfesa ya kera, zai samu kyautar sulallan kudaden intanet da ake kira Ggool da ake iya kashewa a duniyar crypto.
“Zan Iya Hada miliyan N10 Duk Wata”: Bidiyon Wani Dan Najeriya Da Ke Mayar Da Sharar Robobi Su Zama Bulo
Asali: Legit.ng