Osun 2022: Har Yanzun Ba'a Biya Mu Hakkokin Mu Na Aikin Zabe Ba, Jami'an Yan Sanda

Osun 2022: Har Yanzun Ba'a Biya Mu Hakkokin Mu Na Aikin Zabe Ba, Jami'an Yan Sanda

  • Wasu jami'an yan sanda a Osun sun koka kan rashin biyan su Alawus din aikin zaɓe da suka yi tun watan Yuli
  • Yan sandan da abun ya shafa sun yi kira ga Sufeta Janar na ƙasa, Usman Alƙali Baba, ya taimaka ya duba lamarin su
  • Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Osun ta ce bata da masaniyar ba'a biya wasu hakkin su ba

Osun - Wasu jami'an yan sanda karkashin hukumar yan sanda reshen jihar Osun sun koka ranar Laraba cewa har yanzun shiru suke ji game biyan su Alawus ɗin aikin da suka yi a zaɓen gwamnan da ya gabata.

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa an gudanar da zaɓen gwamnan ne ranar 16 ga watan Yuli, 2022, kwanaki 38 kenan da suka gabata, amma har yanzun ba'a biya wasu yan sanda da suka yi aikin tsaro ba.

Kara karanta wannan

Da Taimakon Mutanen Gari, Masu Garkuwa 18 Sun Shiga Komar Yan Sanda a Jihar Arewa

Jami'an, waɗanda suka nemi a ɓoye bayanan su, sun faɗa wa yan jarida a Osogbo ranar Laraba cewa jami'ai 140 daga sashin bincike na jiha (SIB), 30 daga sashin masu kwance bam (EOD), da kusan 160 na MOPOL ba'a biya su ba.

Jami'an yan sanda.
Osun 2022: Har Yanzun Ba'a Biya Mu Hakkokin Mu Na Aikin Zabe Ba, Jami'an Yan Sanda Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ɗaya daga cikin jami'an ya ce baki ɗaya sauran jami'an da suka ba da tsaro lokacin zaɓen sun karɓi alawus din su, har da waɗan da aka turo daga wasu jihohin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ba su zauna haka nan ba, sun yi kokarin jin makasudin rashin biyan su hakkin su amma ba su samu gamsasshen bayani daga hedkwatar yan sanda ba.

Ya ƙara da cewa yi wa doka hawan ƙawara ne gudanar da zanga-zanga kan Alawus, amma ya roki Sufeta Janar na yan sandan ƙasar nan ya taimaka ya duba lamarin su.

Haka zalika, wani jami'in na daban ya ce waɗanda ba'a biya ba mafi yawa suna ƙarƙashin hukumar yan sanda reshen Osun, amma ana tafiyar da komai na su ne karkashin hedkwatar ƴan sanda ta kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Yan Uwan Ɗan takarar Gwamna a Jihar Shugaban Ƙasa

A cewarsa, baki ɗaya yan sandan da ke babban aiki sanye da Kaki da suka yi aiki a zaɓen sun samu alawus ɗin su, inda ya ƙara da cewa ba su san dalilin rashin biyan su ba.

Menene asalin matsalar?

Yayin da aka tuntuɓe ta kan batun, kakakin rundunar yan sandan Osun, Yemisi Opalola, ta ce bata da masaniyar rashin biyan wasu alawus ɗin su na aikin zaɓen.

Ta ƙara da cewa duk jami'in da ba'a biya hakkinsa ba, yana da damar kai kokensa ga hedkwatar yan sanda ta ƙasa.

Hukumar dillancin labarai ta kasa (NAN) ta ruwaito cewa wasu jami'an yan sanda da haka ta faru da su na rashin ba su alawus ɗin zaɓe sun yi zanga-zanga a Osogbo a watan Yuli.

A lokacin mai magana da yawun yan sanda, Muyiwa Adejobi, a wata sanarwa ya ce an samu tsaiko ne daga bankunan jami'an.

Ya ce saɓanin ikirarin wasu daga cikin jami'ai da suka zanta da yan jarida, wasu daga cikin waɗan da aka tura su ba da tsaro a zaɓen Osun, sun samu haƙƙoƙin su tun kafin ranar zaɓe.

Kara karanta wannan

Hotuna: Yan Sanda Sun Fito Zanga-Zanga Kan Rashin Biyan Su Albashi Sama da Watanni 15 a Jihar Arewa

A wani labarin kuma Sojoji Sun Kai Samame Haramtacciyar Kasuwar 'Yan Ta'adda, Sun Hallaka Su Da Dama a Arewa

Sojojin Najeriya na runduna ta 21 sun ragargaji wata haramtacciyar kasuwar ƴan ta'addan Boko Haram da ke Bama a jihar Borno.

Masani kuma mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama, ya ce sojin sun kashe yan ta'adda Shida sun kama gomman su a samamen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262