2023: Ɗan A Mutun Gwamna Wike Ya Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC

2023: Ɗan A Mutun Gwamna Wike Ya Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC

  • Darakta Janar na kungiyar masoyan gwamna Nyesom Wike ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC
  • Hakan ta faru ne yayin da wasu bayanai suka nuna Wike da wasu gwamnonin PDP sun sa labule da Bola Tinubu a Landan
  • Rikicin babbar jam'iyyar hamayya PDP ya kara ɗaukar sabon salo yayin da zaɓe ya rage ƙasa da watanni shida

Rivers - Yayin da rikici ya sake tsananta, Darakta Janar na ƙungiyar magoya bayan Wike, Wike Solidarity Movement, Prince Sudor Nwiyor, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, Nwiyor wanda ya sanar da ficewa daga jam'iyyar a Patakwal, ya kafa hujjar nuna ɓangaranci a jam'iyyar ya sa ya tattara kayansa ya bar PDP.

Gwamnan Ribas, Nyesom Wike.
2023: Ɗan A Mutun Gwamna Wike Ya Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya ƙuma kara da cewa ya sauya sheka ne saboda mutanen da suka yi wa jam'iyyar wahala su ne a yanzu aka maida ba abakin komai ba, kamar yadda leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sabuwar Matsala a PDP, Ɗan Takarar Gwamna Ya Fice, Ya Koma Bayan Wanda Yake So Ya Gaji Buhari a 2023

A cewar tsohon makusancin gwamna Wike, jam'iyya ta koma baiwa sabbin mambobin APC da suka sauya sheka kuɗaɗe domin a yaudare su, su zauna a PDP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa, Nwiyor ya ce:

"Baki ɗaya shugabannin kananan hukumomi 23 na jihar basu mori komai na wani muƙami ba, suna ta tambayar me aka ware musu ne, ban da wata cikakkiyar amsa da zan ba su."
"Wannan dalilin ne ya jawo na yanke hukuncin sauya sheƙa zuwa APC, zan rushe baki ɗaya tafiyar WSM da tsarukanta zuwa jam'iyyar APC."

Wike da wasu gwamnoni sun gana da Tinubu

Wannan cigaba na zuwa a lokacin da wasu rahotanni suka nuna cewa gwamna Nyesom Wike da ke takun saƙa da Atiku Abubakar, ya gana da Bola Tinubu, ɗan takarar APC a Landan.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa wannan ganawar ta sake jefa jam'iyyar PDP cikin ruɗani yayin da ake shirye-shiryen fara kamfe na zaben 2023 da ke tafe ƙasa da watanni shida.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Ƙara Babban Rashi, Na Hannun Daman Ministan Buhari Mai Murabus Ya Koma PDP

A wani labarin kuma Sanata, Yan Majalisun Jiha da Jiga-Jigan PDP Sama da 500 Sun Fice Daga Jam'iyyar

Jam'iyyar YPP reshen jihar Akwa Ibom ta bayyana ɗaruruwan shugabanni da jiga-jigan PDP da suka koma cikinta zuwa yanzu.

Shugaban kwamitin tattara bayanan masu sauya sheƙa, Usenobong Akpabio, ya ce YPP ta kama hanyar nasara a zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262