Buhari Ya Yi Allah-Wadai da Kisan Malami a Yobe, Ya Umarci a Hukunta Jami’in Soja

Buhari Ya Yi Allah-Wadai da Kisan Malami a Yobe, Ya Umarci a Hukunta Jami’in Soja

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayyana bacin ransa da samun labarin kisan gillar da aka yiwa wani malami a Yobe
  • A makon nan ne aka samu rahoton yadda wani sojan Najeriya ya hallaka fitaccen malamin addinin Islama a Yobe
  • Buhari ya umarci a kamo sojan tare hukunta shi, kana ya yi ta'aziyya ga al'ummar jihar da ma gwamnatin Buni

FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu na Najeriya ya yi Allah wadai da kisan wani malamin addinin Islama da wani soja ya yi a jihar Yobe.

Rahotanni a makon nan sun karade kasa game da yadda wani jami'in soja ya hallaka Sheikh Goni Aisami, kuma ya yi yunkurin sace motarsa.

A sanarwar da mai magana da yawun Buhari, Garba Shehu ya fitar, shugaban ya ce wannan kisa abin tausayi ne, kuma ba dabi'ar soja bane kashe mutanen kirki.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Fusata, Ya Bada Umurnin Abin Da Za A Yi Wa Sojan Da Ya Kashe Sheikh Goni Aisami

Buhari ya yi Allah wadai da kashe malamin addini a Yobe
Buhari ya yi Allah-wadai da kisan Malaman Yobe, Ya roki Sojoji da su fatattake masu aikata laifuka | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya kuma ce, halin sojan tabbas ya saba irin horon da rundunar sojin Najeriya ke ba jami'anta, Daily Trust ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban ya kuma umarci hukumomi da su dauki mataki kan wadanda ake zargi da aikata wannan bakin aiki da ma sauran masu aikata laifuka a fadin kasar nan.

Hakazalika, ya yiwa gwamnatin jihar Yobe, al'ummar jihar da dangin mamacin ta'aziyya tare da yiwa Shehin malamin addu'ar rahama, rahoton Vanguard.

Buhari ya ce:

“A horan da aka ba mu, muna bin ka’idojin da suke kyamar irin wannan aika-aika na rashin tunani. Ba ya cikin halayenmu da horonmu mu sanya ’yan kasa da basu ji ba basu gani cikin mawuyacin hali."

Ni Na Kashe Sheik Goni Aisami, Jami'in Soja Da Aka Kama Ya Laburtawa Yan Sanda

A wani labarin, Hukumar Yan sandan a Jihar Yobe, a ranar Talata, ta yi bayanin yadda wani Soja, Kofur John Gabriel, ya halaka Shehin Malami, Goni Aisami, a karamar hukumar Karasuwa ta jihar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: US zata Dawowa Najeriya $23m na Daga Kudin da Abacha ya Handama

Kakakin hukumar, Dungus AbdulKarin, a jawabin da ya fitar yace an damke Gabriel ne tare da abokin aikinsa, Adamu Gideon, dake aiki a 241 Recce Battalion, Nguru, rahoton PremiumTimes.

A cewarsa: "Yayin gudanar da bincike, Sojojin sun amince lallai sun aikata laifin. Har yanzu dai ana bincike kuma suna hannun yan sanda."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.