Da Duminsa: US zata Dawowa Najeriya $23m na Daga Kudin da Abacha ya Handama

Da Duminsa: US zata Dawowa Najeriya $23m na Daga Kudin da Abacha ya Handama

  • Gwamnatocin Najeriya da na Amurka sun kammala yarjejeniyar dawo da $23 miliyan na daga cikin kudin da Sani Abacha ya handama ya kai kasar
  • An kammala yarejejniyar a ofishin ministan shari'a Abubakar Malami da jakadiyar Amurka Mary Beth inda kowanne yasa hannu a madadin kasarsa
  • Kamar yadda Malami ya bayyana, idan an dawo da kudaden za a zuba su kan manyan ayyuka uku na gwamnatin tarayya a kasar nan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Najeriya da gwamnatin Amurka sun kammala yarjejeniyar dawo da sama da $23 miliyan na kudin da Abacha ya handama ya boye a kasar.

Wannan yarejejniyar an sanya hannu kanta ne a ofishin ministan shari'a kuma antoni janar na tarayya, Abubakar Malami, a ranar Talata

A yayin da Malami ya saka hannu a madadin gwamnatin Najeriya, jakadiyar Amurka a kasar Najeriya Mary Beth Leonard, ta saka hannu a madadin gwamnatin Amurkan, Channels TV suka ruwaito.

Kara karanta wannan

Atiku: Sai na mai da jami'o'in tarayya karkashin gwamnatin jiha idan na gaji Buhari a 2023

Kamar yadda Malami yace, idan an dawo da kudaden, za a zuba su a manyan ayyukan gwamnatin tarayya uku da ake yi da suka hada da babban titin Abuja zuwa Kaduna da gadar Niger ta biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel