Fitaccen Mawakin Najeriya Ya Fita Shakatawa da Gwamnonkn PDP Huɗu a Turai

Fitaccen Mawakin Najeriya Ya Fita Shakatawa da Gwamnonkn PDP Huɗu a Turai

  • David Adeleke, wanda ya shahara da sunan Davido, fitaccen mawaki a Najeriya ya haɗu da wasu gwamnonin jam'iyyar PDP a Turai
  • Mawakin ya fita shan abin sha tare da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da wasu gwamnoni uku da ke goyon bayansa
  • Bayanai sun nuna cewa gwamna Wike da yan tawagarsa sun fice Najeriya ne domin gudanar da wasu taruka na dabaru

Fitaccen mawaƙin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido ya haɗu da wasu gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a nahiyar Turai.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa wani Hoton mawaƙin da gwamnonin a zaune ya karaɗe kafafen sada zumunta yanzu haka.

Davido da gwamnoni.
Fitaccen Mawakin Najeriya Ya Fita Shakatawa da Gwamnonkn PDP Huɗu a Turai Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Gwamnonin da Davido ya yi Hoton da su sune; gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai da gwamnan Abiya, Okezie Ikpeazu.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Wike, Ortom Da Wasu Gwamnonin PDP Sun Tafi Turai Ganawa da Tinubu, Majiya

Hotom ya nuna mawakin da gwamnonin zaune suna shakatawa suna shan abin sha amma ba bu tabbacin ranar da mutanen suka haɗu suka gana.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amma jaridar Legit.ng Hausa ta gano cewa gwamnonin babban jam'iyyar Adawa da ke bayan gwamna Wike yanzu haka suna gudanar da tarukan dabara a ƙasar waje.

Kawun Davido ya lashe zaben gwamnan Osun

Kawun Davido, Sanata Ademola Adeleke, shi ne gwamnan jihar Osun mai jiran gado bayan lashe zaɓen da INEC ta gudanar a watan Yuli karkashin inuwar PDP.

Sanata Adeleke ya lallasa gwamna mai ci na jam'iyyar All Progressive Congress APC, Gboyega Oyetola, a zaɓen da aka kammala lami lafiya.

A sakamakon zaɓen wanda babu wata tazara mai yawa, Sanata Adeleke ya samu ƙuri'u 403,371 inda ya lallasa gwamna Oyetola na APC wanda ya tashi da kuri'u 375,027.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Wike Ya Sha Alwashin Ganin-Bayan ‘Yan PDP a Ribas da ke tare da Atiku

Davido ya taka muhimmiyar rawa har kawunsa ya kai ga nasara, kuma tare suka yi faɗi tashi shekaru hudu da suka gabata duk da haƙarsu bata cimma ruwa ba.

A wani labarin kuma Ɗan Majalisar Wakilai ya ce har yanzun batun tsige shugaba Buhari na nan matukar bai magance tsaro ba

Mamban majalisar wakilan tarayya daga jihar Anambra ya ce batun tunbuke shugaba Buhari na nan basu jingine shi ba.

Mr Okwudili Ezenwankwos, ya ce a halin yanzun suna hutu ne da zaran sun koma zasu baje wa'adin da suka ba Buhari a tebur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262