Yunkurin Tsige Shugaba Buhari Na Nan Daram, Ɗan Majalisar Tarayya

Yunkurin Tsige Shugaba Buhari Na Nan Daram, Ɗan Majalisar Tarayya

  • Mamban majalisar wakilan tarayya daga jihar Anambra ya ce batun tunbuke shugaba Buhari na nan basu jingine shi ba
  • Mr Okwudili Ezenwankwos, ya ce a halin yanzun suna hutu ne da zaran sun koma zasu baje wa'adin da suka ba Buhari a tebur
  • Majalisun tarayya sun baiwa shugaban wa'adin makonni ya kawo karshen matsalar tsaro ko ya rasa kujerarsa

Anambra - Mamba mai wakiltar mazaɓar Orumba ta Arewa/Kudu a majalisar wakilan tarayya, Mr Okwudili Ezenwankwos, ya ce majalisun ƙasa ba su jingine batun tsige shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ba.

Ezenwankwo ya jaddada cewa shirin tunɓuke shugaban na nan daram matuƙar Buhari bai lalubo hanyar magance matsalar tsaro, talauci da zaman kashe wando da suka addabi ƙasar nan.

Shirin tsige shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Yunkurin Tsige Shugaba Buhari Na Nan Daram, Ɗan Majalisar Tarayya Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Punch ta rahoto cewa Ɗan Majalisar ya yi wannan furucin ne a Onitcha, jihar Anambra ranar Talata a wurin ƙaddamar da Chambar Lauyoyi mallakin tsohon shugaban NBA reshen Aguata, Chief Clifford Okoye.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Harbe Hadimin Jigon APC Har Lahira a Wurin Shagalin Karin Shekara

Matakin da Majalisa ke cikin kan batun - Ezenwankwo

Ezenwankwo, wanda ya tunatar da cewa NASS na cikin hutu a yanzu, ya ce ƴan majalisu zasu koma bakin aiki a watan Satumba kuma a lokacin zasu duba wa'adin da suka bai wa Buhari.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa ya ce:

"Batun tsige shugaba Buhari lamari ne na gaske saboda batun tsaron lafiya da dukiyoyi shi ne babban aikin farko ga kowace gwamnati kuma shugaban ƙasa ya gaza samarwa al'umma."
"Abun da muke kokarin yi a yanzu muna yi ne domin dawo da ƙasar nan kan turba, idan shugaban ƙasa bai shirya kawo ƙarshen matsalolin tsaro ba, mu kuma a shirye muke mu tsige shi."
"Amma idan muka ga shugaban kasa ya tashi tsaye dagaske a ɓangarensa da sauran yan tawagarsa wajen dawo da zaman lafiya to idan muka koma zamu binne batun tunɓuke shi daga madafun iko."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kakakin Majalisar Kaduna Ya Magantu Kan Shirin Tsige Gwamna El-Rufai

Ɗan majalisar ya kara da tabbatar da cewa matuƙar matsalar tsaro ta cigaba da ci a ƙasar nan, ba zasu yi ƙasa a guiwa ba wajen cire shugaban ƙasa daga kan kujerarsa.

A wani labari na daban kuma Jiga-Jigai da Mambobin PDP Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC, Shugabar mata ta Rungume Su a Kaduna

Shugabar matan jam'iyyar APC a shiyyar kudancin Kaduna ta karɓi sabbin masu sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP.

Mambobin PDP da suka sauya sheka sun bayyana cewa akwai wasu ɗaruruwa da zasu biyo bayan su nan gaba kaɗan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel