Ba Lallai a Yi Zabe a Wasu Jihohin Arewa Maso Yamma Ba, Inji Gwamnonin Najeriya Ga Buhari

Ba Lallai a Yi Zabe a Wasu Jihohin Arewa Maso Yamma Ba, Inji Gwamnonin Najeriya Ga Buhari

  • Gwamnonin Najeriya sun bayyana wasu shawarwari ga shugaban kasa Muhammadu BuahrBuhari domin kawo karshen matsalar tsaro
  • A wani rahoton da muka samo, gwamnonin sun ce ba lallau bane gurbacewar tsaro a Arewa maso Yamma ya bari a yi zaben 2023 ba a yankin
  • Jam'iyyun siyasa da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki na shirin babban zaben 2023 da za a yi nan da watanni biyar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Wani sabon batu ya fito daga bakin gwamnonin Najeriya, inda suka bayyana ra'ayin cewa ba lallai a yi zabuka a wasu jihohin Arewa maso Yammacin kasar nan ba saboda kara dagulewar lamarin tsaro a shiyyar.

Arewa maso Yammancin Najeriya dai ta ta kunshi jihohi bakwai da suka hada da; Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto, da Zamfara.

Kara karanta wannan

Matakin Da Muke Yanzu A Shirin Tsige Shugaba Buhari, Ɗan Majalisar Tarayya Ya Magantu

Ba zai yiwu a yi zabe a wasu jihohi ba, inji gwamnonin Najeriya
Akwai yiwuwar ba za a yi zabe a wasu jihohin Arewa maso Yamma ba, gwamnonin Najeriya ga Buhari | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, gwamnonin sun bayyanawa Buhari hakan ne a wani taron kan samar da wasu ka'idoji.

Takaitaccen bayanin da ke wannan batu na nazari ne ga yanayin tattalin arzikin siyasa, kuma rahoto ne da aka Buhari watan Yulin 2022.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A rahoton da suka mika, gwamnonin sun bukaci Buhari ya gaggauta daukar matakai kan alkawurran da ya dauka na magance matsalar rashin tsaro.

Wasu shawarin da gwamnonin suka bayar

Domin kawo karshen matsalar rashin tsaro, sun shawarci Buhari ya dauki matakin gaggawa, ya kafa sansanin soji a Birnin Gwari, Rijana, Kachia da Mararraban Jos a jihar Kaduna da Kontagora da Gwada a jihar Neja.

Sun kuma shawarci Buhari ya sake nazari kan zabin abokin takarar da Bola Tinubu na APC, da kuma tasirinsa wajen kawo kada kuri’an 'yan yankin Arewa maso Yamma da kuma makomar APC, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Tuban Turji: 'Yan Najeriya Sun yi Martani, Suna Zargin Akwai Lauje Cikin Nadi

A bangare guda, sun kuma nemi a duba sakamakon zaben fidda gwanin jam'iyyar APC, PDP da NNPP da aka gudanar a watannin baya.

Irin Mulkin da Muka Yi a Borno da Legas, Shi Za Mu Yiwa Najeriya, Inji Abokin Takarar Tinubu

A wani labarin, abokin takarar Tinubu a zaben 2023, Kashim Shettima ya bayyana irin tagomashin da suka shiryawa 'yan Najeriya, Channels Tv ta ruwaito.

Shettima ya ce, abubuwan mamaki da Bola Tinubu ya yi jihar Legas sadda yake gwamna su ne za su kasance a Najeriya bayan 2023.

Hakazalika, ya ce za su surka da irin ababen da ya yiwa jihar Borno, domin ganin an samu ci gaba a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

iiq_pixel