Mutumin da Ya Kirkiri Na’urar Sarrafa Toroso Ya Yi Bayani, Yana Neman Hannun Jari

Mutumin da Ya Kirkiri Na’urar Sarrafa Toroso Ya Yi Bayani, Yana Neman Hannun Jari

  • Wani fasihi dan kasar Koriya ta Kudu ya yada labarinsa a kafar yanar gizo bayan da ya kirkiri wani nau'in bandaki da ke juya toroso zuwa makamashi
  • Makamashin da na'urar ke samarwa na iya daukar wutan gida guda. A yanzu dai yana biyan mutane, musamman dalibai wani nau'in kudin crypton da ya kirkira mai suna Ggool ga duk wanda ya totsa toroso a kai
  • Ya zuwa yanzu dai wannan fasaha tasa ta fara samun kalubale saboda gwamnatin kasar ta cire masa tallafin da ta saka, amma duk da haka Cho Jae-weon na alfahari da fasaharsa

Kasar Koriya ta Kudu - Wani farfesan kasar Koriya ta Kudu masi suna Cho Jae-weon ya ba da mamaki yayin da ya kirkiri wata na'urar sarrafa toroso.

A halin yanzu, farfesan toroso ya ce yana fuskantar kalubalen gaske kasancewar gwamnati ta cire masa tallafi a fasahar tasa mai suna BeeVi, wacce ke sauya toroso zuwa makamashi daga nan kuma zuwa kudin intanet

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Karamar Yarinya Ta Yi Suman Karya Bayan Mahaifiyarta Ta Kama Ta Tana Fentin Bandaki

Duk wanda ya yi amfani da wannan nau'in bandaki na juya toroso da farfesa ya kera, zai samu kyautar sulallan kudaden intanet da ake kira Ggool da ake iya kashewa a duniyar crypto.

Yadda wani ya kirkiri na'urar da ke sarrafa toroso zuwa abu mai amfani
Mutumin da Ya Kirkiri Na’urar Sarrafa Toroso Ya Yi Bayani, Yana Neman Hannun Jari | Hoto: indianexpress.com
Asali: UGC

An ce yawancin masu amfani da wannan bandaki dai dalibai ne, kuma da gaske suna samun na kashewa ta hanyar totsa toroso a bandakin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani rahoton jaridar Reuters ya ce, an kaddamar da wannan bandaki ne a watan Yulin 2021 ga al'ummar duniyar crypto da sauran al'ummomi masu sha'awar kayan zamani.

A da gwamnatin kasar Koriya ne daukar nauyin wannan aiki, amma a yanzu, rahoto ya ce gwamnati ta cire hannunta, lamarin da ya kawo cikas ga ci gaban wannan aiki na farfesa Cho.

Amfanin wannan bandaki

A wata hira da Cointelegraph, Cho, ya yi tsokaci game da amfanin wannan fasaha tasa, inda ya bayyana cewa, ya kamata duniya ta kalli wannan kokarin a matsayin nasara duk da shawarar da gwamnatin ta yanke na janye hannunta.

Kara karanta wannan

“Zan Iya Hada miliyan N10 Duk Wata”: Bidiyon Wani Dan Najeriya Da Ke Mayar Da Sharar Robobi Su Zama Bulo

Yace:

“Fasahar tasa da tsarin FSM na iya kawo sauyi gagarumi kuma mai kyau a cikin al'umma idan aka dabbaka shi."

Ya kuma bayyana cewa, wannan fasaha za ta taimakawa birane wajen samar da haske maimakon kawai mutane su yi toroso ya zame musu jangwan wajen debe shi da jigilar tsatface muhalli.

Cho ya kuma yin karin haske da cewa, fasaharsa da kuma sinadarin methane da take samarwa za su iya amfani wajen samar da dumi ko kuma girki.

Wata 'yar Najeriya ta nuna yadda take sana'ar POP, jama'a sun shiga mamaki

A wani labarin, wata 'yar Najeriya mai suna Okeke Stephanie, ta ba da mamaki yayin da ta bayyana irin sana'ar da take yi don samun na kashewa.

Stephenie dai 'yar jihar Delta ce, kuma ta ce ta kama sana'ar daben saman daki na POP ne domin ta kashe kwarkwatar da ke kanta.

Ta kuma bayyana cewa, ta kan sha suka da zolaya game da wannan aikin da take yi, inda wasu ke cewa aiki ne na maza.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da tankin ruwa ya fadon kan wani gida, ya danne mutane

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.