Magidanci Ya Yi Karar Surukarsa A Kotun Shari'ar Musulunci Kan 'Ƙin Dawo' Masa Da Matarsa Saboda Bashi Da Kudi

Magidanci Ya Yi Karar Surukarsa A Kotun Shari'ar Musulunci Kan 'Ƙin Dawo' Masa Da Matarsa Saboda Bashi Da Kudi

  • Wani mutum mazaunin Rigasa a Kaduna ya yi karar mahaifiyar matarsa a kotun shari'a saboda ta hana matar komawa gidansa
  • Zainab Mohammad, wacce aka yi karar ta shaidawa kotu cewa ta hana yarta komawa gidan mijin ne saboda ba ya kulawa da lafiyarta da ciyarwa
  • Zainab ta kuma fada kotu cewa sai mijin ya biya ta kudin da ta kashe na tiyata a asibiti da ciyarwa na wata tara kafin matar ta koma

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Wani dan kasuwa, Ismaila Ibrahim, a ranar Talata, ya yi karar wata Zainab Muhammad, surukarsa a kotun shari'a da ke Rigasa Kaduna, saboda kin yarda matarsa ta koma gidan aure, NAN ta rahoto.

Mai shigar da karar, mazaunin layin Police Station a Rigasa, ya shaidawa kotu cewa wanda ya yi karar ta ki yarda matarsa ta koma gidansa ne saboda halin rashin kudi da ya ke ciki.

Kara karanta wannan

So Nake su Koyi Sana'a da Tattali: Mata Mai Gidan Gona ta ba Yaranta Aiki, Albashinsu 105k a Sati

Kotun Musulunci
Magidanci Ya Yi Karar Surukarsa A Kotun Shari'ar Musulunci Kan 'Ƙin Dawo' Masa Da Matarsa Saboda Bashi Da Kudi. Hoto: @daily_nigerian.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ina kaunar matata kuma ina son ta dawo gida, ina rokon kotu ta taimaka min matata ta dawo gida," in ji shi.

Martanin surukar magidancin

A bangarenta, wanda aka yi karar ta ce ta hana yarta komawa gidan mijin ne saboda rashin kulawa.

Ta ce an yi wa yarta tiyata yayin haihuwa kuma jinjirin ya rasu.

Ta kara da cewa wanda ya shigar da karar ya gaza biyan kudin asibiti kuma ya yi watsi da matar a gidan iyayenta na watanni uku babu kulawa, rahoton Vanguard.

Kalamanta:

"Ya tawo bayan watanni uku, yana neman a dawo masa da matarsa ni kuma na ce zai ta yi wata shida a hannu na domin ta murmure sosai.
"Ya ta tayi rashin lafiya bayan tiyatan kuma ni na biya dukkan kudin asibitin da ciyarwa."

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Karamar Yarinya Ta Yi Suman Karya Bayan Mahaifiyarta Ta Kama Ta Tana Fentin Bandaki

Ta ce a shirye take ta mika wa mijin matar idan zai biya kudin da ta kashe kan magani da ciyarwa na wata tara.

Martanin alkali

Mai shari'a, Abubakar Salisu-Tureta, ya daga cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 4 ga watan Satumba domin wanda aka yi karar ta gabatar da lissafin dukkan kudin da ta kashe kan yarta.

Kaduna: Ana Rikici Kan Katifa Tsakanin Miji Da Mata Da Ke Son Kashe Aurensu A Kotun Shari'a

A wani rahoton, wata kotun shari'a a Kaduna, a ranar Litinin ta umurci wata mata mai neman saki, Halima Ahmad ta mayar da katifa ga mijinta da suka kwance alaka, Suleiman Atiku.

Mr Atiku, ma'aikacin hukumar gyaran hali, tunda farko ya bukaci a dawo masa da katifansa, kafin ya amince da bukatar sakinta, The Cable ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164