Ba Zamu Yarda Ba, A Gaggauta Hukuncin Sojojin Da Suka Kashe Sheikh Aisami, JIBWIS
- Ƙungiyar Izala ta ƙasa ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta hukunta sojojin da suka ƙashe Malaminta a jihar Yobe
- Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya ce IZALA ba zata yarda irin wannan ta'addancin ba kuma zasu zuba ido su ga matakin da mahukunta zasu ɗauka
- Wani Soja da ya nemi Sheikh Goni Aisami ya rage masa hanya, ya kashe Malamin har lahira yayin da ya tsaya biyan buƙata
Abuja - Ƙungiyar Jama'atul Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) wacce aka fi sani da IZALA ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta hukunta waɗan da suka kashe Sheikh Goni Aisami Gashuwa a jihar Yobe.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a shafinta na Facebook, shugaban ƙungiyar na ƙasa, Sheikh Dakta Abdullahi Bala Lau, ya bukaci gwamnati ta ɗauki mataki kan sojoji guda biyu da suka kashe Malamin ƙungiyar.
Bala Lau ya kuma yaba wa rundunar yan sanda reshen jihar Yobe bisa ɗaukar matakin damƙe sojojin da aka samu a tare ga gawar Marigayin bayan faruwar lamarin.
Bayanai sun nuna cewa Malamin na kan hanyarsa ta komawa gida Gashuwa daga Kano yayin da wani Soja ya nemi ya rage masa hanya zuwa Jaji-Maji, ƙaramar hukumar Karasuwa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai Sojan wanda ke ɓoye da mummunar manufa ya harbe Sheikh Goni har lahira yayin da ya tsaya domin biyan buƙata.
Rahoto ya nuna cewa sakamakon zuwan yan Banga ne suka gano akwai wani abu da ya faru, nan take suka sanar da ƴan sanda, waɗan suka zo suka damƙe sojojin guda biyu.
Ba zamu amince da wannan ta'addancin ba - Sheik Bala Lau
Da yake martani, Bala Lau ya ce Izala ba zata amince da irin wannan ta'addancin kan malaman ta ba, "Mun zura ido da kunnuwa domin sauraron yadda zata kaya wajen hukunta su cikin gaggawa."
Shugaban IZALA ya kuma miƙa ta'aziyya a madadin ƙungiya ga iyalan marigayin, ɗaukacin al'ummar Gashuwa da jihar Yobe da ma ƙasa baki ɗaya bisa rashin Sheikh Goni Aisami.
Ya kuma yi addu'ar Allah maɗaukakin sarki ya karɓi shahadarsa, ya kyautata makwancinsa, ya sa Aljannar Furdausi ta zama makomarsa da sauran Musulmai baki ɗaya.
A wani labarin kuma Hukumar Sojin Najeriya Ta Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Kisan Sheikh Goni a Jihar Yobe
Hukumar Sojin Najeriya ta kafa kwamiti wanda zai gudanar da bincike Kan musabbabin kisan Malami a Yobe.
Ana zargin wasu Sojoji guda biyu da hannu a kashe babban Malamin, Sheikh Gonu Gashua, ranar Jummu'a da daddare.
Asali: Legit.ng