Hukumar Soji Ta Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Kisan Sheikh Goni a Yobe

Hukumar Soji Ta Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Kisan Sheikh Goni a Yobe

  • Hukumar Sojin Najeriya ta kafa kwamiti wanda zai gudanar da bincike Kan musabbabin kisan Malami a Yobe
  • Ana zargin wasu Sojoji guda biyu da hannu a kashe babban Malamin, Sheikh Gonu Gashua, ranar Jummu'a da daddare
  • Hukumar Sojin ta ce zata binciko bayanan sojojin da ake zargi kuma zasu fuskanci fushin doka daga karshe

Yobe - Hedkwatar sashi na 2 na Rundunar Operation Haɗin Kai ta hukumar sojin Najeriya ta kafa kwamitin da zai gudanar da bincike kan zargin hannun wasu sojoji a kisan Sheikh Goni Gashua a jihar Yobe.

A wata sanarwa da ta fitar ta hannun ɗaya daga cikin kakakinta, Kaftin Kennedy Anyanwu, hukumar sojin ta ce a halin yanzun tana kan bincike don gano cikakkun bayanan Sojojin.

Sheikh Goni Gashua.
Hukumar Soji Ta Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Kisan Sheikh Goni a Yobe Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Jaridar Premium Times ta ruwaito yadda aka cafke Sojoji biyu bisa zargin kisan babban Malamin addinin Musuluncin.

Kara karanta wannan

Hotunan Motar Sheikh Goni Aisami da Wasu Sojoji Suka Kashe Don Sacewa

Sheikh Goni ya rasa rayuwarsa ne hannun wasu mutane a kusa da Jaji Maji, ƙaramar hukumar Karasuwa a jihar Yobe, ranar Jummu'a da daddare.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Yobe, Dungus Abdulkareem, wanda ya tabbatar da lamarin ga jaridar, ya ce, "Nan da ƴan kwanaki za'a bayyana cikakken abun da ya faru ga al'umma."

Wane mataki hukumar Sojojin Najeriya ta ɗauka?

Da take tabbatar da lamarin, rundunar Sojin Najeriya ta ayyana kisan Malamin da babban abun takaici da dana sani, "Duk da rashin sassauci kan take doka da ƙa'idojin aikin soji."

Channels tv ta ce a sanarwan da ta fitar ranar Lahadi, Rundunar sojin ta ce:

"Sashin sojin tare da haɗin guiwar hukumar yan sanda reshen jihar Yobe sun duƙufa bincike domin gano cikakkun bayanan Sojojin da ake zargi."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Harbe Hadimin Jigon APC Har Lahira a Wurin Shagalin Karin Shekara

"Bugu da kari sashin Sojin ya kafa kwamitin bincine da zai bankaɗo duk wani abu Mai alaƙa da lamarin mara daɗi, kuma daga ƙarshe za'a miƙa Sojojin su fuskanci dokar hukumar soji da ta fararen hula."

A wani labarin kuma Yan Sanda Sun Kai Samame Sansanin Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sule Dawa, a Jihar Katsina

Dakarun yan sanda sun kai samame sansanin yan bindiga a kauyen Anguwan Mai Zuma, ƙaramar hukumar Ɗanja a Katsina.

Rundunar yan sanda ta ce yayin samamen, Jami'ai sun sheke ɗan ta'adda ɗaya, sun kwato kayan aikin su da yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel