Yadda Ma’aikatan Gwamnati a Najeriya Suke Karyar Mutuwa Domin a Ba Su Kudin Fansho
- Hukumar fansho a Najeriya ta bayyana yadda tsoffin ma'aikata ke shirya mutuwar karya saboda su karbi fansho
- An sha samun lokuta a cewar PenCom, da ma'aikata ko danginsu ke gabatar da takardun karya na mutuwa
- Ba bakon abu bane a Najeriya gwamnati ta rike fanshon ma'aikata, wannan yasa wasu ke neman mafita
FCT, Abuja - Hukumar fansho ta kasa ta bayyana fushinta game da yadda ma'aikatan gwamnati masu ritaya da dangin da ke ba da rahoton mutuwar karya domin tunkarar gwamnati da sunan karbar kudin fansho.
Hukumar ta ce za ta dauki matakai masu tsauri kan wadannan mutane kamar yadda doka ta tanada, rahoton Punch.
PenCom ta dauki matakin cewa, bayan gabatar da shaidar mutuwa gareta, dole ne bankuna su rufe asusun mamaci domin tabbatar da ya mutu kafin a fara maganar hakkinsa na hannun hukumar.
Hukumar ta ce ta damu matuka da yadda ake yawan samun mutuwar karya daga tsoffin ma'aikata da danginsu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shugaban sashen hakkokin ma'aikata da inshora a PenCom, Obiora Ibeziako, ne ya bayyana damuwa yayin da yake zantawa kan yadda ake karbar hakkokin ritaya da kudaden fanshon ma'aikata.
Ya ce:
"’Yan Najeriya sai mutuwa suke suna dawowa. Idan ka turo mana da sanarwar ka mutu, za mu tabbatar da hakan ta hanyar sanar da bakinka su garkame asusunka.
“Muna ganin yadda mutane ke mtuwar karya; muna ganin yadda ma’aurata ke karyar mutuwar abokan rayuwarsu lokacin da PFAs suka fara bin tsarin da ya dace.
"Kai, an samu wani yanayi, ana cikin duba yadda za a ba da hakkin wani mamaci, sai gashi ya shigo. Matarsa tuni ta samo shaidar mutuwa na bogi, kuma shi ake bukata a yi komai tunda mutumin an ce ya mutu."
Ya kara da cewa:
“Akwai wani lokaci kuma, muka kira mutumin ya ce tabbas, shi ya shirya mutuwarsa saboda yana da bukatar kudi.
Hakazalika, an sha samun korafe-korafe daga tsoffin ma'aikata cewa, danginsu sun bi sun karbe dan abin da suka tara na fansho.
Matsi ke sa mutane yin haka watakila, inji tsohon ma'aikaci
Wakilin Legit.ng Hausa ya tattauna da wani tsohon maa'aikacin gwamnati a jihar Gombe, wanda ya bayyana yadda ya sha fama kafin fara fitar kudadensa.
Mallam Ibrahim Muhammad, wanda tsohon malamin makaranta ne ya bayyana cewa, ya yi ritaya a shekara 2008, kuma ya sha fama kafin kudin fanshonsa su fara fita.
A cewarsa:
"A lokacin na cire rai, domin bansan ya zanyi ba. Duk inda ka taf ana son ka ba da cin hanci. Wasu tare kuka yi aiki, amma ka zama abun banza a idonsu.
"To, a tunani na wannan karya ta mutuwa tana da nasaba da halin ko in kula na su kansu ma'aikatan fanshon da kuma kula da tsoffin ma'aikata."
Mallam Adamu Umar, tsohon ma'aikacin shari'a ya ce:
"Gwamnati na da matsala idan aka zo bangaren kula da tsohon ma'aikaci. Jihohi nawa kake jin an rike fanshon ma'aikata? irin wannan ke jawo tunin aikata ba daidai ba."
Ma’aikata Sun Yi Zanga-Zangar Rashin Biyansu Albashin Shekaru 5 a Kuros Riba
A wani labarin, jaridar PM News ta ruwaito cewa, ma’aikatan gwamnati akalla 1,700 ana jihar Kuros Riba suka fito zanga-zanga a yau Talata 23 ga watan Agusta don nuna damuwa da rashin samun albashi na tsawon shekaru biyar.
An ce 'yan zanga-zangar sun taru ne a sakateriyar jihar tun da karfe 7:30 na safe kuma sun mashigarta ga ma'aikata.
An ga rubuce-rubuce a jikin kwalaye da alluna, inda suke bayyana irin kin amincewarsu da ta hanyar rera wakoki cikin fushi.
Asali: Legit.ng