Allah Ya Yiwa Kauran Katsina Kuma Hakimin Rimi, Nuhu Abdulkadir, Rasuwa
- Masarautar Katsina ta wayi gari da wani babban rashi na daya daga cikin manyan mambobinta
- Kauran Katsina kuma Hakimin Rimi, Alhaji Nuhu Abdulkadir, ya kwanta dama a yau Talata, 23 ga watan Agusta
- Marigayin ya dan yi fama da rashin lafiya kuma yanzu haka ana nan ana shirye-shiryen jana'izarsa
Katsina - Allah ya yiwa daya daga cikin manyan yan majalisar masarautar Katsina, Alhaji Nuhu Abdulkadir, rasuwa.
Jaridar PM News ta rahoto cewa, marigayin wanda ya kasance Kauran Katsina kuma Hakimin Rimi ya rasu a safiyar ranar Talata, 23 ga watan Agusta, a gidansa da ke karamar hukumar Rimi.
Basaraken ya rasu yana da shekaru 77 a duniya.
Marigayin ya dan yi fama da yar gajeriyar rashin lafiya jim kadan bayan bikin cikarsa shekaru 40 a kan karagar mulkin Rimi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daya daga cikin iyalansa, Alhaji Aminu Nuhu-Abdulkadir ne ya tabbatar da rasuwarsa.
Za a yi jana’izarsa a yau daidai da koyarwar addinin Musulunci, domin yanzu haka ana nan ana shirye-shiryen sada shi da gidansa na gaskiya, jaridar Leadership ta rahoto.
Ko Shakka Babu Zan Auri Mace Fiye Da Daya, Basarake Mai Shekaru 19
A wani labarin kuma, Oba Oloyede Adeyeoba Akinghare ll Arujale Ojima na Okeluse, da ke karamar hukumar Ose ta jihar Ondo ya ce zai aure mace fiye da kuda daya kamar yadda al’ada ta tanadar.
Sarkin mai shekaru 19 wanda ya kammala makarantar sakandare kwanan nan, ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Vanguard.
Basaraken ya bayyana cewa auren mace fiye da guda daya wajibi ne ga duk mutumin da ya zama sarki saboda matarsa ta fari idan ta haifi namiji shine zai zama sarki nag aba sannan dan mata ta biyu ya zama abun da ake kira Eleki.
Asali: Legit.ng