Tuban Turji: 'Yan Najeriya Sun yi Martani, Suna Zargin Akwai Lauje Cikin Nadi
- 'Yan Najeriya da yawa sun sha mamakin labarin tuban shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, da ya fito daga bakin mataimakin gwamnan Zamfara
- Wasu sun zarga cewa, yana son amfani da jami'an tsaron Najeriya ne wurin yakar abokan hamayyarsa, daga baya ya sake kafa daularsa
- Wasu kuwa caccakar mataimakin gwamnan suka dinga yi inda suke cewa ya bar 'yan bindigan su yi magana da hukumomin da suka dace
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Zamfara - 'Yan Najeriya sun dinga martani kan rahoton dake bayyana cewa gagararren 'dan bindiga Bello Turji, wanda ya saba kashewa da garkuwa da jama'a a Sokoto da Zamfara ya tuba.
Idan za a tuna, a watan Disamban 2021, shugaban 'yan bindigan ya rubuta wasika zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Gwamna Bello Matawalle da Sarkin Shinkafi kan yana so a tsagaita da ruwan wuta.
A yayin jawabi a wani taro a Gusau a ranar Lahadi, mataimakin gwamnan jihar, Hassan Nasiha, ya bayyana cewa Turji ya tuba kuma ya rungumi matakan zaman lafiya na gwamnatin jihar.
Nasiha yace Turji ya tuba kuma hakan ya dawo da zaman lafiya a kananan hukumomin Birnin Magaji, Shinkafi da Zurmi a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda yace, Turji yanzu halaka 'yan bindigan da basu tuba yake ba, masu addabar jama'a a kananan hukumomin Shinkafi, Zurmi da Birnin Magaji a jihar.
'Yan Najeriya sun yi martani
Wannan ikirarin bai zauna a kwakwalwar 'yan Najeriya da kyau ba. nan take suka fara martani inda kowa ke hasashe da hango abinda zai iya sa Turji ya tuba haka dare daya.
@KawuGarba, yace wannan ikirarin tuban wani salo ne da Turji ya bullo da shi domin amfani da jami;an tsaro wurin sake kafa daularsa tare da yakar 'yan adawarsa.
Yace:
"Abun takaici ne yadda gwamnatin jihar Zamfara ta bada wata damar sasanci da Bello Turji, shugaban 'yan bindigan da ake nema ido rufe. Zai yi amfani da jami'an tsaronmu domin ya yaki kungiyoyin da basu ga maciji kuma ya kafa daularsa daga baya. Ba wannan bane karo na farko da hakan ta faru."
@sarnchos, yace mataimakin gwamnan ya bar 'dan ta'addan yayi magana da kansa mana.
"Me yasa mataimakin gwamnan Zamfara ke magana a madadin 'yan bindigan? A bar 'yan bindigan su dinga magana da sojoji a maimakon haka."
Gaskiya ta Fito: Sojan da Ya Halaka Sheikh Aisami an Sauya Masa wurin AIki ne Saboda Yayi wa Kwamanda Sata
A wani labari na daban, sojan da aka kama kan zargin halaka fitaccen malamin addinin Islama a jihar Yobe, Goni Aisami, an sauya masa wurin aiki ne sakamakon sace N480,000 da yayi wa kwamandansa.
Sojan mai suna John Gabriel, mai mukamin Lance Corporal, yana aikin sojan ne da bataliya da 241 Recce dake Nguru, kuma an kama shi ne matsayin wanda ake zargi da sace N80,000 da N400,000 a lokuta daban-daban kafin a mayar da shi kan titi, wata majiyar sojoji tace.
Gaskiya ta Fito: Sojan da Ya Halaka Sheikh Aisami an Sauya Masa wurin AIki ne Saboda Yayi wa Kwamanda Sata
Sojan shi ne dogarin kwamandan bataliyar, GS Oyemole, mai mukamin kanal kafin a sauya masa wurin aiki a watan Yuli saboda muguwar dabi'arsa, majiyar da ta sanar da Premium Times ta tabbatar.
Asali: Legit.ng