'Yan Bindiga Sun Sheke Babban Sojan Najeriya a jihar Anambra
- Miyagun 'yan bindiga a jihar Anambra sun sheke soja mai mukamin Manjo a yankin Azia dake karamar hukumar Ihiala
- Yankin Azia yana daga cikin yankuna masu matukar hatsari a jihar inda aka gano matattarar 'yan ta'adda ne a jihar
- Tuni abokan Manjo Churchill Orji suka dinga ta'aziyyarsa tare da mika lamurran jihar ga Ubangiji kan kamarin da ta'addanci yayi
Anambra - Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun halaka sojan Najeriya wanda aka bayyana sunansa da Manjo Churchill Orji a yankin Azia mai matukar hatsari na karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, Orji ya fito daga kauyen Nneogida na Agulu dake karamar hukumar Anaocha ta jihar. Har yanzu dai a ba a san abinda ya kai shi Azia ba wanda ake kallo da wuri mafi hatsari a jihar.
'Dan makarantarsu Orji a sakandare mai suna Leonard Edu, yayin jajantawa kan mutuwar sojan Najeriya, yace gaba yake da shi a makarantar sakandare ta yara maza dake Agulu.
"Suna cikin shugabannin dalibai a wancan lokacin. Da gaske ne 'yan bindiga sun halaka shi a Azia duk da har yanzu ba mu samu cikakken labarin abinda yayi sanadiyyar mutuwarsa ba," Edu yace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun bayan mutuwarsa, abokan Orji sun dinga martani a soshiyal midiya.
A ta'aziyyar daga cikin abokan, yace:
"Ubangiji yayi maka rahama 'dan uwana daga kauyen Nneogidi, Agulu, Manjo Churchill Orji wanda aka kashe a jiya Lahadi a Azia/Ukpor yayin bai wa kudu maso gabas kariya daga miyagu."
Wani ya rubuta:
"Ubangiji, muna karkashin ikonka a jihar Anambra. Ina fatan ka yi wa Manjo C. Orji Rahama."
Daily Trust ta rahoto cewa, a yayin da ta tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, yace har yanzu bai samu rahoto kan aukuwar lamarin ba.
Ihiala tana da iyaka da jihar Imo, inda aka ruwaito cewa an halaka manjon, kuma yankin yayi kaurin suna da lamurran ta'addanci.
Yadda 'Yan Bindiga Sun Kallafawa Manoman Kaduna Harajin Miliyoyin Naira
A wani labari na daban, manoman karamar hukumar Birnin Gwari dake jihar Kaduna sun amince zasu biya makuden kudaden da 'yan bindiga suka kallafa musu in har suna son amfani da gonakinsu.
Kamar yadda Ishaq Usman Kasai, shugaban kungiyar masarautar Birnin Gwari, yace 'yan bindigan sun kallafa musu harajin miliyoyin naira kan manoman, Daily Trust ta ruwaito.
A wata takarda, yace manoman sun sun yanke hukuncin yin ciniki da 'yan bindigan saboda basu da wata mafita.
Yace noma a yankin ya gurgunce a Birnin Gwari da sama da kashi saba'in na yadda suka saba a lokacin da suke iya zuwa gonakinsu a shekaru uku da suka gabata.
Asali: Legit.ng