Hukumar NDLEA Ta Kama Miyagun Kwayoyi Miliyan 2.3 da Aka Shirya Kawo Wa Arewa

Hukumar NDLEA Ta Kama Miyagun Kwayoyi Miliyan 2.3 da Aka Shirya Kawo Wa Arewa

  • Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kame wasu haramtattun kayayyaki da aka shirya kai wa Arewa
  • Hukumar ta NDLEA na kara kamari wajen shigo da miyagun kwayoyi a zagayen jihohin Najeriya
  • Hukumar ta bayyana adadin kayan da ta kama, da kuma mutanen da ke da hannu wajen shigo da wadannan kayayyaki

FCT, Abuja - NDLEA, hukuma mai yaki da shia da safarar miyagun kwayoyi ta kame tarin miyagun kwayoyi na opioids da sauran kayan buguwa da suka haura miliyan 2.3 da aka nufi kai wa jihohin Arewa.

Wannan na fitowa ne daga bakin kakakin hukumar, Femi Babafemi a wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi 22 ga watan Agusta, Channels Tv ta ruwaito.

Ya bayyana cewa, jihohin da za a kai kayayyakin su ne kamar haka: Borno, Kano, Kaduna, Sokoto, Zamfara, Gombe, da Nasarawa.

Kara karanta wannan

Kudin Haya 2.7m duk shekara, Kudin Diesel N80k: Bidiyon Gidan Mai Dakuna 3 Da Budurwa Ta Gani A Lagas

Humumar NDLEA ta kame miyagun kwayoyi da aka shirya kai wa jihohin Arewa
Hukumar NDLEA Ta Kama Miyagun Kwayoyi Miliyan 2.3 da Aka Shirya Kawo Wa Arewa | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya kuma bayyana cewa, an kame miyagun kwayoyi ne a yankunan Kaduna, Kogi, Sokoto, da kuma babban birnin tarayya Abuja a makon da ya gabata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda aka kama kayayyakin

A ranar 12 ga watan Agusta, an kama Umar Sanusi a wani samame a Kaduna, an kuma mai dashi Kano inda aka kama shi da katan 50 na pregabalin mai girman 300mg da ke dauke kwayoyi 750,000, masu nauyin kilogiram 375.

Hakazalika, an kama kwalabe 7,068 a Akuskura da aka shirya kai wa Kaduna, Zamfara, Gombe, Kano da Borno.

A hannun wani Abubakar Ahmad a Zamfara, an kama kwalabe 285 na NPS a ranar 13 ga watan Agusta, rahoton Daily Trust.

A jihar kogi kuma, an kama kwayoyi 696,000 na Tramadol da Exol-5 da aka dauko daga Anambra inda za a zarce da su jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya a ranar 19 ga watan Agusta

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku Da Wike: PDP Za Ta Rasa Mambobi Da Dama A Yayin Da Jerry Gana Yayi Barazanar Fita Daga Jam'iyyar

A ranar 19 ga watan Agusta, hukumar ta kame 300,000 na Diazepan a kan titin Okene zuwa babban birnin tarayya Abuja a hannanun wani Faruku Bello mai shekaru 30 a ranar 17 ga watan na Agusta.

A babban birnin tarayya Abuja da wasu a jihar Anambra, an kama kwayoyin 323,200 masu girman 225mg da aka yi niyyar kai wa jihar Nasarawa da ke makwabtaka da Abuja.

NDLEA ta gano Tramadol na N22bn bayan kama attajiri abokin harkallar Abba Kyari

A wani labarin, hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta ce binciken da ake yi kan wani attajiri mai suna Afam Mallinson Emmanuel Ukatu, ya kai ga gano kwayoyin tramadol fiye da na Naira biliyan 22.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da wayar da kan jama'a na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ranar Talata a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan ta'addan ISWAP sun sace manoma a gonakinsu a jihar Borno

Babafemi ya ce binciken ya kai ga gano yadda wanda ake zargin a watan Oktoban 2019 ya shigo da kwantena biyu cikin Najeriya, dauke da katan 1,284 na Tramadol da darajarsa ta kai sama da Naira biliyan 22.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.