NDLEA ta gano Tramadol na N22bn bayan kama attajiri abokin harkallar Abba Kyari

NDLEA ta gano Tramadol na N22bn bayan kama attajiri abokin harkallar Abba Kyari

  • Hukumar NDLEA ta yi nasarar gano wasu boyayyun batutuwa da ke kunshe da harkallar kwayar Abba Kyari
  • Wannan na fitowa ne bayan da hukumar ta kama wani da take zargi da hannu a shigo da miyagun kwayoyi
  • Hukumar ta yi bayani, ta ce ta gano yadda attajirin ke shigo da miyagun kwayoyi ba bisa ka'ida ba zuwa Najeriya

FCT, Abuja - Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta ce binciken da ake yi kan wani attajiri mai suna Afam Mallinson Emmanuel Ukatu, ya kai ga gano kwayoyin tramadol fiye da na Naira biliyan 22.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da wayar da kan jama'a na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ranar Talata a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya rigamu gidan gaskiya

Yadda aka gano mutumin dake harkallar kwaya da Abba Kyari
NDLEA ta gano Tramadol na N22bn bayan kama attajiri abokin harkallar Abba Kyari | Hoto: ejesgist.com
Asali: Facebook

Babafemi ya ce binciken ya kai ga gano yadda wanda ake zargin a watan Oktoban 2019 ya shigo da kwantena biyu cikin Najeriya, dauke da katan 1,284 na Tramadol da darajarsa ta kai sama da Naira biliyan 22.

Ya ce an yi wannan bayanin ne domin dakile cece-kucen da wasu ke yi na cewa NDLEA ba ta da wata hujja ta kama Afam, wanda duniya ta sani a matsayin shugaban rukunin wasu kamfanoni.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, bayan shafe watanni ana sa ido akansa, Afam ya kama hanyarsa ta zuwa Abuja a bangaren MM2 na tashar jirgin saman Legas, Ikeja, a ranar Laraba, 13 ga Afrilu.

A cewarsa:

“Bincike ya nuna cewa shi babban mai shigo da manyan kayayyaki ne na iri daban-daban da kuma yawan alluran Tramadol Hydrochloride, masu girman 120mg, 200mg, 225mg da 250mg, duk haramtattu.

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

“Ya mallaki kamfanonin sarrafa magunguna da robobi, wadanda ya ke amfani da su wajen fakewa da shigo da miyagun kwayoyi cikin Najeriya.

“Hukumar ta ce a ci gaba da bincike kan harkallar Tramadol din N3bn tsakanin wanda ake zargin da tawagar Abba Kyari ta IRT, jami’an ta sun kara gano wasu shaidu."

A cewar Babafemi, wanda ake zargin yana shigo da kwayoyin Tramadol fiye da yadda aka amince a shigo dasu Najeriya, kamar yadda Economic Confidential ta tattaro.

Ya kara da cewa:

"Babu shakka nan ba da jimawa ba wanda ake zargin zai gurfana a gaban kotu."

NDLEA ta kama attajirin da ya kulla harkallar kwaya da Abba Kyari ta N3bn

A wani labarin, hukumar NDLEA ta samu nasarar kame Afam Mallinson Emmanuel Ukatu, wani attajirin da ake zargin yana da hannu a harkallar safarar miyagun kwayoyi ta DCP Abba Kyari da tawagarsa.

Sanarwar da NDLEA ta fitar ta bayyana cewa Afam na da hannu dumu-dumu a harkallar shigo da miyagun kwayoyi na N3bn da ke da alaka da Abba Kyari.

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

Bayan shafe watanni ana sa ido akansa, an kama Mista Ukatu wanda shi ne shugaban Kamfanin Mallinson Group of Companies, a cikin jirgin da zai je Abuja daga filin jirgin saman Legas, Ikeja a ranar Laraba 13 ga Afrilu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel