Wasu Tsagerun ’Yan Bindiga Sun Sheke Jigon APC Kazeem Kekere a Jihar Osun
- Jigon APC a jihar Osun ya bakunci kiyama yayin da wasu 'yan bindiga suka bi shi suka farmake a jiharsa
- Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, Kazeem Kekere ya kasance shugaban kungiyar NURTW ta masu harkar sufuri
- Shugaban karamarsu ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma bayyana yadda 'yan ta'addan suka aikata kisan gillan
Jihar Osun - Wani jigon APC a jihar Osun mai suna Kazeem Kekere a Apomu dake karamar hukumar Isokan ya bakunci lahira a wani sabon harin 'yan bindiga.
Rahoton da muka samo daga jaridar The Nation na cewa, an bindige jigon na APC ne a jiya Asabar 20 ga watan Agusta cikin dare lokacin da 'yan bindigan suka tarfa shi.
An ce Kazeem ne shugaban kungiyar ma’aikatan harkar sufuri ta kasa (NURTW) reshen Apomu ta karamar hukumar Isokan a jihar.
Majiyar ta bayyana cewa, Kazeem ya yi amfani da kujerarsa a lokutan zabe wajen nuna goyon baya ga jam'iyyar APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar majiyar:
“An kashe shi ne tsakanin karfe 8 zuwa 9 na dare a tsakanin yankin Oke-Alfa da Timberland, a wani rafi da ke yankin.
"Wasu motoci biyu ne suka bi shi zuwa wurin. Motocin sun tarfa shi har ta kai motarsa ta kauce daga nan aka kashe shi.
Shugaban karamar hukumar Isoka, Tajudeen Bello ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma lallai 'yan bindiga ne suka bindige shi, rahoton Daily Sun.
Hakazalika, jaridar ta ce ta samu tabbacin faruwar lamarin daga bakin shugaban APC, Prince Gboyega Famodun.
Shugaban na APC ya bayyana hakan ne ta bakin hadiminsa a bangaren yada labarai, Kola Olabisi.
A bangaren jami'an tsaro, rahoto ya ce har yanzu dai rundunar 'yan sanda ba ta ce komai ba kan wannan mummunan aiki.
'Yan Bindiga Sun Sace Wasu Jiga-Jigan Jam’iyyar APC a Jihar Imo
A wani labarin, a jiya Asabar 20 ga watan Agusta ne wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC biyu tare da kashe wasu mutum uku a jihar Imo.
Rahoton da muka samo daga jaridar Daily Trust ya ce tsagerun sun mamaye wani sahshe sashe ne na Amaraku-Orji, kan sabuwar hanyar Owerri zuwa Okigwe da aka gyara kwanan nan, kuma sun shafe wani adadi na sa’o’i suna cin karen ba babbaka.
Rahoton ya ce, an sace Mr Aloy Onuekwusi, wanda aka ce shi ne mai Diamond Pools a jihar ta Imo. Hakazalika, an kashe wani wani mutum da aka ce direban wanda aka ruwaito direba ne ga daya daga cikin jiga-jigan na APC da aka sace.
Asali: Legit.ng