Dan kasuwa ya toshe al'aurarsa saboda bai san ya sake haihuwa bayan samun 'yaya 5

Dan kasuwa ya toshe al'aurarsa saboda bai san ya sake haihuwa bayan samun 'yaya 5

  • Saboda tsadar kudin makaranta, wani marubuci kuma dan kasuwa ya tafi asibiti toshe al'aurarsa
  • Aita Joel wanda ya wallafa littafi kwanan nan kan kasuwanci yace kudin makarantan na firamare kadai yanzu $5000
  • Daga yanzu Aita Joel ba zai sake haihuwa a rayuwarsa ba, amma yana da 'yaya biyar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Uganda - Wani attajiri dan kasar Uganda, Aita Joel, ya sanar da duniya cewa ya tafi asibiti don a cire masa jijiyar al'aurarsa bayan samun haihuwar 'yaya biyar da matarsa.

Tsinke jijiyar al'aura wacce aka fi sani da 'Vasectomy' a turance wani abu aikin tiyata da likitoci ke yiwa mutum ta hanyar tsinka jijiyar dake tafiyar da maniyyin namiji zuwa mafitsara.

Duk namijin da aka yiwa ba zai yi yiwa mace ciki ba har abada.

Aita Joel ya bayyana cewa an yi masa wannan aiki ne ranar Juma'a inda ya saki hoton a shafinsa na Tuwita.

Kara karanta wannan

Harin Jirgin kasa: 'Dan Uwan Budurwar da Shugaban Yan Bindiga Ke Kokarin Aurawa Kansa Ya Koka

Aitaa
Dan kasuwa ya toshe al'aurarsa saboda bai san ya sake haihuwa bayan samun 'yaya 5 Hoto: @aitajoel
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabin da ya saki, yace dalilin toshe haihuwarsa shine don ya mayar da hankali kan 'yayansa biyar yadda ya kamata.

A cewarsa:

"Bayan haihuwan 'yaya 5, na yanke shawarar kawo karshen haihuwa don basu rayuwa maikyau."
"Idan kana son baiwa 'yayanka Ilimi mai kyau, sai ka biya kudin makaranta mai kyau. Musamman yadda wasu makarantun firamare ke karban kudin makaranta milyan 20 (N3.2m) a zango."

Asali: Legit.ng

Online view pixel