Yadda Matukan Jirgin Sama Suka Bingire da Bacci Suna Tsaka da Tuka Fasinjoji

Yadda Matukan Jirgin Sama Suka Bingire da Bacci Suna Tsaka da Tuka Fasinjoji

  • Wasu matukan jirgin sama biyu sun dinga bacci suna tsaka da tuka fasinjojin da suka kwaso daga kasar Sudan
  • A ranar 15 ga watan Augusta, jirgin ya tasi daga Khartoum inda zai sauka a Addis Ababa dake Habasha amma sadarwa ta katse baki daya da jirgin
  • Tuni dai jirgin ya sauka bayan mintuna 15 kuma kamfanin Ethiopian Airlines ya dakatar da matukan har sai an kammala bincike

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Matukan jirgin sama har su biyu sun bingire da bacci, hakan yasa ba su sauka da wuri ba a yayin da suka kwaso fasinjoji daga Sudan zuwa kasar Habasha a ranar Litinin, kamar yadda rahoton Aviation Herald ta bayyana.

Lamarin ya faru ne a jirgin Kamfanin Ethiopian Airlines mai lamba 737-800 wanda ya taso daga Khartoum zai je Addis Ababa, jaridar Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Na Yi Alkawarin Kuɗi N50,000 Ga Duk Wanda Ya Fallasa Bayanan Yan Bindiga a Jihata, Gwamnan APC

Pilot Fell Asleep
Yadda Matukin Jirgin Sama Ya Bingire da Bacci Yana Tsaka da Tuka Fasinjoji. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

Bayanai da aka samu daga shafin yanar gizon ya bayyana cewa, jirgin na tafe ne da nisan kafa 37,000 lokacin da ya gaza sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Addis Ababa Bole inda zai sauka a ranar 15 ga watan Augusta.

Masu kula da tafiyar jiragen dake kasa sun kasa samun matukan jirgin bayan kokarin da suka dinga na ganin sun yi magana.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai, jirgin ya bayyana alama bayan da ya wuce inda zai sauka kuma ya cigaba da tafiya.

Jirgin saman a hankali ya fara sauka zuwa kasa sannan ya karasa sauka bayan kusan mintuna 25 daga lokacin da ya dace ya sauka.

"Mun samu rahoto wanda ya bayyana cewa, jirgi mai lamba Et343 da ya taho daga Khartoum zuwa Addis Ababa ya katse sadarwa da masu kula da jirgin na kasa dake a Addis Ababa a ranar 15 ga Augustan 2022," takardar da Ethiopian Airlines ta fitar ranar Juma'a tace.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Matashi Yayi Ido Biyu da Mahaifinsa Yana Kama Dakin Otal da Wata Mata

“Daga bisani jirgin ya sauka bayan dawowar sadarwa tsakanin matukan da masu kula na kasa. An dakatar da matukan daga aiki har sai a na kammala bincike.
"Za a dauka matakin gyara wanda ya dace bayan sakamakon binciken ya fito," takardar tace.

Matsiyata Kawai: Fasto Yayi wa Masu Bauta Tatas Bayan Sun Gaza Siya Masa Agogo Mai Tsada

A wani labari na daban, wani fasto daga garin Missouri dake Amurka yayi suna bayan bidiyonsa ya bayyana inda yake caccakar masu bauta kan yadda suka gaza siya masa agogon Movado mai matukar tsada.

A wa'azinsa, Fasto Carlton Funderburke na cocin Well dake Birnin Kansas, an ji a bidiyo yana sukar mambobin cocin inda yake kiransu da fatararru.

Babu shakka bidiyon ya janyo martani kala-kala a yanar gizo inda wasu ke alakanta shi da zama faston bogi wanda ya fito tatsar kudaden masu zuwa coci.

Kara karanta wannan

Matsiyata Kawai: Fasto Yayi wa Masu Bauta Tatas Bayan Sun Gaza Siya Masa Agogo Mai Tsada

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng