Da duminsa: 'Yan Bindiga Sun Kaiwa Matar Gwamna Mummunan Farmaki
- Miyagun 'yan bindiga sun budewa tawagar matar gwamnan Osun, Kafayat Oyetola, wuta a daidai kasuwar Owode dake jihar Osun
- Lamarin ya faru wurin karfe 8 na daren Juma'a yayin da matar gwamnan ke hanyarta ta zuwa garin Osogbo inda miyagun suka dinga harbi
- Ganau ya tabbatar da cewa, wani direban babbar mota ne ya tare musu hanya, lamarin da ya kawo fada tsakanin jami'an tsaronta da wasu 'yan bindiga
Osun - A yammacin Juma'a, wasu da ake zargin miyagun 'yan bindiga ne sun kai wa tawagar uwargidan gwamnan jihar Osun, Kafayat Oyetola, mummunan farmaki, jaridar Vanguard ta rahoto.
Duk da har yanzu babu bayanai masu yawa kan harin, majiyoyi a Owode dake Ede, inda lamarin ya auku sun ce tawagar matar gwamnan ta nufi Osogbo ne kuma wurin kasuwar Owode 'yan bindigan suka bude mata wuta wurin karfe 8 na dare.
Wani mazaunin yankin wanda ya bayyana sunansa da Alayande, ya sanar da jaridar Punch cewa wata babbar mota ce ta samar da cunkoso lokacin da tawagar matar gwamnan ta isa kasuwar Owode.
"Ana ta kokarin ganin direban babbar motar ya matsar da ita, hakan yasa aka samu hargitsi tsakanin jami'an tsaronta da direban.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Naji harbin bindiga babu adadi a inda nake tsaye. Wurin akwai duhu amma tabbas rikici aka yi da jami'an tsaronta da wasu 'yan bindiga," yace.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola har yanzu bata yi martani kan sakonnin kar ta kwanan da aka aike mata ba.
Amma jami'ar yada labarai ta ofishin mata gwamnan, Oluwatunmise Iluyomade, ta tabbatar da aukuwar farmakin.
Ta ce:
"Ba a rasa ko rai daya ba a farmakin. Wasu jami'an tsaron lafiyar matar gwamnan ne suka samu miyagun raunika."
‘Yan Bindigan da Suka Dauke Fasinjojin Jirgin Kasa na Shirin Aure ‘Yar shekara 21
A wani labari na daban, Tukur Mamu ya bada sanarwar cewa ‘yan bindiga na shirin auren wata daga cikin fasinjojin jirgin da aka sace a hanyar Abuja-Kaduna.
The Cable ta ce Alhaji Tukur Mamu wanda na-kusa ne da Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana haka a ranar Juma’a, 19 ga watan Agusta 2022.
Yayin da yake bada sanarwar sakin wasu mutane hudu a jiya, ‘dan jaridar ya fadakar da mutane cewa ‘yar autar da ke tsare ta na fuskantar barazana.
Asali: Legit.ng