Bidiyon Amarya Da Ango Suna Sharban Kuka Wiwi A Wajen Liyafar Bikinsu

Bidiyon Amarya Da Ango Suna Sharban Kuka Wiwi A Wajen Liyafar Bikinsu

  • Bidiyon wani ango da amaryarsa suna kuka da hawaye a wajen liyafar bikinsu ya yadu
  • A cikin bidiyon wanda ya yadu a soshiyal midiya, an gano sabbin ma’auratan zaune a kujera suna ta zubar da hawaye
  • An gano wasu mata biyu kusa dasu suna ta rarrashinsu yayin da suke share hawayen da kyallen zani

Najeriya – Wani bidiyo na wani ango da amaryarsa suna kuka wiwi da hawaye a wajen biyafar bikinsu ya haifar da zazzafar martani a shafukan soshiyal midiya.

Ma’auratan sun tsima zukata yayin da aka gano su zaune kusa da junansu suna zubar da hawayen murnar ganin wannan rana mai cike da tarihi a rayuwarsu.

Amarya da ango
Bidiyon Amarya Da Ango Suna Sharban Kuka Wiwi A Wajen Liyafar Bikinsu Hoto: arewafamilyweddings
Asali: Instagram

Angon ne ya fara fashewa da kuka yayin da amaryar da ke zaune kusa dashi ta taya shi.

A cikin bidiyon wanda shafin arewafamilyweddings ya wallafa a Instagram, an gano wasu mata biyu zaune a gefen kowannensu suna aikin rarrashinsu yayin da suke goge idanunsu da kyallen zani.

Kara karanta wannan

Basa Taba Koyon Darasi: An Hasko Jami’an Yan Sanda Suna Karban Na Goro Daga Fasinjoji, Bidiyon Ya Yadu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

munarhs_delight_ ta ce:

"@twentyone_ten dole kayi ko a fasa."

mustee_sadeeq ya ce:

Naga alamar kukan nan shi mah al'ada ne..ka tanadi kyallen zaninka

hafsatruwansanyii ta yi martani:

"Hmmmm Allah mana zabi mafi Alkhairi Ameen."

princess_khardeejah

"❤️❤️❤️ MashaAllah Allah ya kaimu ranar nawa."

fhaty_m ta yi martani:

"Ya Allah ga fatima gare ka ❤️."

Ayyiriri: Yariman Jordan Mai Jiran Gado Zai Angwance Da Kyakkyawar Amaryarsa ‘Yar Saudiyya, Hotuna

A wani labarin, Yariman kasar Jordan mai jiran gado, Hussein bin Abdullah II zai angwance da budurwarsa ‘yar kasar Saudiya, Rajwa Khaled Al-Saif.

Jaridar Zawya ta rahoto cewa an yi baikonsu a ranar Laraba, 17 ga watan Agusta, kamar yadda Kotun masarautar Hashemite ta Jordan ta sanar.

An yi bikin baikon ne a gaban mai martaba sarkin Jordan, Abdullah II, Sarauniya Rania da kuma yan uwan amaryar a garin Riyadh ta kasar Saudiya.

Kara karanta wannan

Soyayyar Gaskiya: Bidiyon Auren Kyakkyawar Doguwar Amarya da Wadan Angonta ya Janyo Cece-kuce

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng