Gwamnatin Najeriya da Ta Gombe Za Su Kafa Makarantun Almajiri Guda 3 a Gombe

Gwamnatin Najeriya da Ta Gombe Za Su Kafa Makarantun Almajiri Guda 3 a Gombe

  • Gwamnatin Najeriya, ta Gombe da bankin raya Muslunci sun hada kai domin gina makarantun Almajirai a Gombe
  • Za a fara koyawa Almajirai Turanci da Larabci domin su zama 'yan kasa na gari kuma su daina yawo sakaka
  • Gwamnatin Najeriya ta bayyana aniyar mayar da yaran da ba sa zuwa makaranta zuwa azuzuwa domin inganta ilimi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Gombe - Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar Bankin Raya Musulunci da Gwamnatin Jihar Gombe, sun ce za su kafa makarantun Almajiri na kwana guda uku a jihar.

Babaji Babadidi, shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Gombe (SUBEB) ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Gombe ranar Alhamis.

Ya ce za a gina makarantun ne a Dogonruwa, Gombe ta Kudu, Garin Hardo, Gombe ta tsakiya da Tudun Wada duk dai a Gombe ta tsakiya, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Goro a miya: Gwamnoni sun taru a Aso Rock don tattauna batun tattalin arziki, Buhari bai halarta ba

Gwamnati za ta gina manyan makarantun almajirai a Gombe
Gwamnatin Najeriya za ta kafa makarantun Almajiri guda 3 a Gombe | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Shugaban ya ce harsunan da za a ke koyarwa a makarantun za su kasance Larabci, Turanci da sauran harsunan da aka fi amfani da su a yankin kamar Hausa ko Fulfulde.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, kafa makarantun zai taimaka wajen inganta yawan dalibai a makarantu, da rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, da kuma wayar da dalibai su koyi sadarwa da sanin bayanai.

Yadda ginin zai kasance

Babadidi ya ce gwamnatin jihar ta kuma amince da gina makarantar allo ta Almajirai a unguwar Yulunguruzu da ke cikin babban birnin jihar.

Ya ce a cikin ginin za a samar da irin kayan aikin da ake bukata kuma ake samu a duk makarantun zamani da ke fadin jihar.

Shugaban ya ce za a gwamutsa ilimin Boko da tsarin makarantun allo da makarantun gargajiya domin samar da sakamako mai kyau.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Hare-hare sun munana, an garkame dukkan makarantu a Jigawa

A cewar Babadidi:

“Hakki ne da ya rataya a wuyan gwamnati ta samar da ilimi ga kowace irin al’umma; ba ma so su rika yawo ba tare da karatun Boko ba.
"Muna son Almajirai su samu ilimin addinin Islama da na Boko domin su zama 'yan kasa nagari a gobe."

Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

A wani labarin, Goodluck Ebele Jonathan ya ce gwamnatinsa ta kawo wannan shiri ne domin ganin an cusa ilimin zamani a cikin manhajar karatun musulunci.

Jaridar Daily Trust ta rahoto tsohon shugaban kasar yana cewa sun yi hakan ne da nufin daliban su samu aiki, sannan kuma a magance matsalar rashin tsaro.

Dr. Jonathan ya bayyana wannan a ranar Litinin, 7 ga watan Fubrairu 2022, yayin da yake jawabi a wajen wani taro a kan ilmi da aka shirya a jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

Ku Nemi Taimakon Ubangiji Kan Al'amuran Siyasarmu, IBB Ga 'Yan Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel