Yan Sanda Sun Kai Samame Matattaran Bata-Gari A Abuja, Sun Fatattake Su Sun Kona Wurin Kurmus
- Jami'an rundunar yan sandan Najeriya a Abuja sun kai hari wani matattaran bata gari da ke Dawaki Zone 7 inda suka fatattaki bata garin suka kona wurin
- Wani dan sanda cikin tawagar wadanda suka kai sumamen ya ce da isarsu wurin bata garin suka fara tserewa da suka hango su hakan yasa suka kone wurin kurmus bayan isarsu
- Kakakin yan sandan birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh ta tabbatar da kai harin inda ta ce yana cikin wani mataki da yan sandan suke dauka don fatattakar masu laifi daga Abuja
Abuja - Tawagar yan sanda da ta hada da rassa biyar a birnin tarayya Abuja, a daren ranar Laraba sun kona wata mabuyar yan ta'adda a Dawaki Zone 7 na Abuja bayan bata garin da ke zama a wurin sun tsere bayan hango yan sandan.
The Punch ta rahoto cewa bata gari da ke adabar mutanen Dawaki da Dutsen Alhaji a Abuje ne ke zama a wurin.
Wani mazaunin unguwar wanda ya nemi a boya sunansa ya ce mabuyar ne matattaran bata gari, yana mai cewa mutanen gari suna tsoron bi ta wurin musamman da dare.
Jami'an yan sanda daga Dawaki, Zuba, Kubwa, Bwari da Dutse Alhaji ne suka kai harin karkashin jagorancin DPO SP Ali Johnson.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wani dan sanda, wanda ya nemi a boye sunansa ya ce an kona wurin ne domin hana bata gari taruwa kuma su mayar da wurin sansanin masu laifi.
Ya ce:
"Bata garin sun cika wandunansu da iska bayan sun hango mu. Hakan yasa ba mu da wata zabi sai kona wurin."
Kakakin yan sandan Abuja ta yi karin haske
Da ta ke tsokaci kan lamarin, mai magana da yawun yan sanda na Abuja, Josephine Adeh, ta ce atisayen na cikin kokarin da rundunar ke yi na kawar da laifuka a birnin tarayya.
Adeh ta ce:
"Muna lalata duk wani matattaran bata gari da nufin fatattakar masu laifi daga birnin tarayya Abuja.
"Mun kai samame wurin domin yana iya sauyawa ya zama matattaran masu laifi."
'Ni Na Rika Yi Wa Yan Bindiga Magani,' Fasinjar Jirgin Kaduna Da Ya Samu Yanci Ya Magantu
A wani rahoton, Mustapha Imam, daya daga cikin mutanen da yan bindiga suka sace jirgin kasar Kaduna zuwa Abuja ya ce ya yi wa yan bindiga magani a lokacin da ya ke tsare a hannunsu.
A wani bidiyon da Tukur Mamu, mawallafin Desert Herald wanda ya taimaka wurin tattaunawa don ganin an sake su, fasinjan ya bayyana zamansa a hannun yan bindigan a matsayin 'lamari matukar muni'.
Asali: Legit.ng