Hotunan Yadda Aka Kori Wani Sojan Ruwan Najeriya Daga Aiki Saboda Aikata Badala

Hotunan Yadda Aka Kori Wani Sojan Ruwan Najeriya Daga Aiki Saboda Aikata Badala

  • Rundunar sojin ruwan Najeriya ta kori wani jami'in da ta gurfanar saboda aikata l*wadi da wani yaro
  • Bayanan kotun soji sun bayyana cewa, an kama jami'in ne da aikata wasu laifuka hudu da suka saba tarbiyyar aiki
  • Hotunan da muka samo sun nuna lokacin da jami'in ke tube kayan aikinsa a daidai sadda yake sallama da aikin

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, rundunar sojin ruwan Najeriya ta sallami wani jami'inta bayan gano yana yunkurin aikata luwadi.

Rundunar ta kori SLT VN Ukpawanne bisa zargin aikata laifin da wani matashi a jihar Delta.

An gurfanar da Ukpawanne ne a kotun soji kuma alkali ya same shi da laifuka wasu laifuka hudu.

An kori sojan ruwan Najeriya daga aiki saboda aikata luwadi
Hotunan yadda aka tsige wani sojan ruwan Najeriya saboda aikata badala | Hoto: Punch Newspaper
Asali: Facebook

Laifukan da jaridar ta ruwaito ya aikata sun hada da kin bin doka da oda, yunkurin aikata luwadi, rashin kunya da kuma amfani da miyagun kwayoyi.

Kara karanta wannan

Kotun Saudiyya Ta Yankewa Daliba Hukuncin Shekaru 34 a Magarkama Kan Amfani da Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Laifukan da aka ce ya aikata sun sabawa doka karkashin sashe na 57, 95; 93; 65 (1) na AFA CAP A20 LFN 2004.

Rahoton Leadership ya bayyana cewa, an kuma yanke masa daurin watanni shida, karin wasu watanni shidan da kuma zaman gidan yari na shekara daya ga dukkan laifuffukan guda hudu da ya aikata a lokaci guda.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta bayyana cewa:

"Jami'in da aka koran a halin yanzu yana jiran izinin likita daga Cibiyar Kula da Lafiya ta Sojin Ruwa kafin a mika shi ga Cibiyar Gyaran Hali ta Sapele don fara zaman gidan kaso."

Kotu ta yanke wa yan luwadi hukuncin kisa a jihar Bauchi

A wani labarin, babbar kotun shariar musulunci dake jihar Bauchi ta yanke wa wasu matasa biyu da dattijo hukuncin kisa ta hanyar jefewa ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022. bisa laifin yiwa wasu kananan yara luwadi.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Nake Hana Mijina Damar Saduwa da Ni, Matar Aure Ta Faɗa Wa Kotu

Al’amarin ya faru ne a karamar hukumar Ningi kamar yadda jaridar BBC hausa ta rawaito. Kotun ta samu mutanen, wanda suka hada da matasa biyu da kuma wani dattijo mai misalin sheakru 70, da wannan kazamin laifi, wanda dukkanin su suka amsa aikata lafin.

Sai dai wani ma’aikacin kotun, ya shaidawa BBC hausa cewa babu wani lauya da ya wakilci wadanan mutanen a yayin zaman shari’ar, da kotun ta yanke hukunci ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.