Kotun Saudiyya Ta Yankewa Daliba Hukuncin Shekaru 34 a Magarkama Kan Amfani da Twitter

Kotun Saudiyya Ta Yankewa Daliba Hukuncin Shekaru 34 a Magarkama Kan Amfani da Twitter

  • Kotun Saudi Arabia ta garkame matashiya shekaru 34 a gidan yari bayan an kama ta da laifin nemawa mata hakki a Twitter
  • Salma Al-Shebab daliba ce dake karatun digirin digirgir din ta a jami'ar Leed dake Ingila kuma tana da yara biyu maza
  • An fara yanke mata hukuncin shekaru shida da farko amma an sake mata hukuncin shekaru 34 bayan ta daukaka kara

Saudi Arabia - Wata dalibar jami'ar Leeds mai suna Salma al-Shebab mai shekaru 34 wacce ta dawo daga Ingila bayan hutun da taje, ta shiga hannun hukuma kuma aka yanke mata hukuncin shekaru 34.

An yanke mata wannan hukuncin nan ne sakamakon amfani da asusunta na Twitter da kuma bibiya tare da sake wallafa maganganun masu rajin kare hakkin mata.

Mahaifiyar yara biyun ana zarginta da amfani da Twitter wurin tada tashin-tashina da tada tarzoma tare da karantsaye ga tsaron kasa bayan ta yi wallafa kan hakkin mata a Saudi Arabia.

Kara karanta wannan

Ke duniya: Hotunan yadda aka kori jami'in sojin ruwan Najeriya daga aiki saboda aikata luwadi

Saudi Student
Kotun Saudiyya Ta Yankewa Daliba Hukuncin Shekaru 34 a Magarkama Kan Amfani da Twitter. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

The Daily Mail ta rahoto cewa, Al-Shebab, wacce take da yara maza kanana biyu masu shekaru hudu da shida, an fara yanke mata hukuncin shekaru shida amma kotun ta'addanci ta Saudi a ranar Litinin ta kara mata zuwa shekaru 34 bayan ta daukaka karar hukuncinta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kara da haramta mata tafiya na tsawon shekaru 34 bayan ta kammala zaman gidan kasonta.

Al-Shebab ta shiga hannun hukuma a watan Janairun 2021 yayin da take hutu a Saudi Arabia bayan ta kammala shirinta na komawa Ingila, inda take yi digirin digirgir a jami'ar Leeds.

An tattaro cewa, a yayin yanke hukunci, kotun ta alakanta amfani da soshiyal midiya da Al-Shebab take yi wurin taimakon yada goyon bayan hakkin mata a Saudi Arabia da kuma nuna kara ga mata da aka garkame saboda neman hakkin mata kamar Loujain Al-Hathloul, da kuma neman masu 'yanci.

Kara karanta wannan

Batanci Ga Annabi: Kotu Ta Bada Umurnin Sake Shari'ar Aminu Yahaya-Shariff, Wanda Aka Yanke Wa Hukuncin Kisa a Kano

An kama ta ne bayan ta sake wallafa wata wallafa da da 'yar uwar Al-Hathloul, Lina ta yi.

Rashin Kudin Jirgi: Matashi Zai Tafka Asarar Daukar Nauyin Karatunsa Na N16m da Jami'a Tayi a Amurka

A wani labari na daban, Smart Godwin Micah, wani dalibin Najeriya wanda ya samu gurbin karatu domin yin digirinsa na biyu a Physics a jami'ar North Carolina dake Durham, USA.

Smart ya samu gurbin karatun kuma an dauka nauyin karatunsa kacokan mai darajar naira miliyan 16.

Sai dai, Smart ya gaza samun kudin tafiya da wanda zai fara karatunsa saboda a halin yanzu bashi da ko tikitin jirgin tafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel