Batanci Ga Annabi: Kotu Ta Bada Umurnin Sake Shari'ar Aminu Yahaya-Shariff, Wanda Aka Yanke Wa Hukuncin Kisa

Batanci Ga Annabi: Kotu Ta Bada Umurnin Sake Shari'ar Aminu Yahaya-Shariff, Wanda Aka Yanke Wa Hukuncin Kisa

  • Kotun daukaka kara ta bada umurnin a sake yin shari'ar mawaki Aminu Yahaya-Shariff wanda aka yanke wa hukuncin kisa saboda batanci da ya yi ga Annabi (SAW) cikin wakarsa
  • Kotun daukaka karar ta bada wannan umurnin ne kan dalilin cewa an samu wasu matsaloli yayin shari'ar na farkon ciki har da rashin bawa wanda aka gurfanar lauya da zai kare shi
  • Kuma kotun daukaka karar ta tabbatar da cewa kundin tsarin shari'ar musulunci na 2000 ta Jihar Kano ba ci karo da kundin tsarin mulkin kasa ba don haka ya halasta a yi aiki da shi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Kotun daukaka kara da ke zamanta a Jihar Kano ta yi watsi da karar da aka shigar kan hukuncin babban kotu, ta kuma bada umurnin sake shari'ar mawaki Aminu Shariff Yahaya, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zan gyara fannin ilimi cikin wata shida idan na gaji Buhari, inji wani dan takara

Kotun ta jaddada cewa dokar shari'ar Jihar Kano ta Penal Code bai ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya ba.

Yahaya Shariff
Batanci Ga Annabi: Kotu Ta Yi Watsi Da Daukaka Karar Aminu Sharrif, Ta Umurci A Sake Shari'ar. @daily_trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da ya ke yanke hukuncin ranar Laraba, Mai sharia Abubakar Mu'azu Lamido ya ce kudin tsarin mulkin kasa ya bawa jihohi yin dokoki ta hannun majalisun jiha, Vanguard ta rahoto.

Ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ta yadda da damar zaben kowanne addini amma bawa jihohi damar su zabi wani addini ya zama na jihar ba.

Yahaya, wanda da farko aka yanke wa hukuncin kisa a kotun shariah a Kano a watan Agustan 2020, ya roki kotun babban kotun jihar ta soke hukuncin da aka masa na kisa.

Dalilin soke shari'ar da ta zartar da hukuncin kisa kan mawaki Aminu Yahaya-Shariff

Babban kotun na Kano, a watan Nuwamban 2020, ta soke hukuncin kotun shari'ar kan dalilan cewa wanda ake zargin ba a bashi lauya mai kare shi ba, sannan ta ce a sake shari'ar.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dalibin kwaleji ya yI barazanar sace 'Provost', ya shiga hannun hukuma

A bangarensa, Aminu, ta bakin lauyansa Kola Alapinni, ya roke kotun ta tabbatar da wasu abubuwa biyu.

Batutuwan biyu, a cewar takardun kotun sune, "Ko alkalan babban kotun sunyi dai-dai da suka umurci a sake shari'ar a maimakon sallamar wanda ake zargin da watsi da matakin kotun shari'ar.
"Na biyu, ko babban kotun ta yi dai-dai a yayin da ta ayyana cewa dokar shari'a ta Penal Code na Jihar Kano na 2000 bai saba wa dokar kasa ba."

A hukuncin da alkalan uku suka yi, Mai sharia Lamido da B.M. Ugo wanda suka fi bada mafi yawan hukuncin sun jadada hukuncin babban kotun na cewa a sake sharia a maimakon rashin amincewa da hakan da alkali na uku ya bada.

A dokar shari'a ta Penal Code na 2000, an tanadi hukuncin kisa ga batanci musamman ga manzon tsira Annabi Muhammad (SAW), wanda shine laifin da ake zargin Aminu da aikatawa.

Kara karanta wannan

Shawari kyauta: Hanyoyi 15 da za ku bi domin kiyaye kanku daga fadawa matsala a Najeriya

Zainab: Yadda Aka Kashe Min Mijina Musulmi Mahaddacin Alkur'ani Kan Zargin Zagin Annabi

A wani rahoton, Zainab, matar ma'aikacin sintiri Ahmad Usman wanda aka kashe shi a unguwar Lugbe, Abuja kan zargin yin batanci ga Manzon Allah (SAW) ta ce mijinta mahhadacin Alkur'ani ne kuma sharri aka masa.

Ta bayyana hakan ne cikin hirar BBC Hausa ta yi da ita yayin ziyarar da wakilin ta ya kai gidansu marigayi Ahmad.

Rahoton ya nuna Zainab tana takaba kuma tana dauke da juna biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164