Abinci Da Aka Dafa Da Paracetamol Na Iya Lalata Hanta, Likita Ya Yi Gargadi

Abinci Da Aka Dafa Da Paracetamol Na Iya Lalata Hanta, Likita Ya Yi Gargadi

  • Akwai masu dafa abinci da magungunan zamani, sai dai, masana sun ce irin wannan girki na kawo matsala
  • Paracetamol musamman, wani likita ya ce akwai matsalar hanta da maganin ke iya kawo duk mai amfani dashi
  • Girka fatan dabbobi na daya daga cikin abincin da ke bukatar lokaci kafin dahuwa, wannan yasa ake neman mafita

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani kwararren likita mai suna Dr. Chinonso Egemba, ya gargadi yan Najeriya a kan cin abincin da aka dafa da maganin paracetamol, yana mai cewa irin wannan abinci na iya haifar da gagarumin matsala.

Dr. Egemba, wanda aka fi sani da ‘Aproko Doctor’ a soshiyal midiya ya yi gargadin cewa shan paracetamol fiye da ka’ida na iya haifar da matsalar cutar hanta, jaridar Punch ta rahoto.

Ya bayyana hakan ne a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Instagram mai suna @aproko_doctor.

Kara karanta wannan

Shiga siyasa: Matasa a Abuja sun kama wani Bishap, sun lakada masa dukan tsiya

Abinci
Abinci Da Aka Dafa Da Paracetamol Na Iya Lalata Hanta, Likita Ya Yi Gargadi Hoto: Punch
Asali: UGC

A cewar likitan, ana yawan amfani da paracetamol ka ciwon kai, ciwon jiki da zazzabin shawara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, ya bayyana cewa wasu gidajen abinci a kasar suna amfani da paracetamol wajen dafa nama, da tunanin cewa zai taimaka wajen sa naman ya yi laushi.

Ya bayyana cewa ainahin sinadarin da ke cikin paracetamol shine “acetaminophen”, yana mai cewa idan aka dafa wannan sinadarin yana iya tabarbarar da lafiyar cikin dan adam.

Ya ce:

“Wasu gidajen cin abinci na taimakawa wajen rashin lafiyar da ke damunmu a Najeriya. Suna amfani da paracetamol da ke maganin ciwon kai da zazzabi wajen dafa nama sboda sun ji cewa yana sawa ya yi laushi.
“Ainahin sinadarin paracetamol “acetaminophen” ne kuma daya daga cikin abubuwan da yake haifarwa idan aka sha ba bisa ka’ida ba shine ciwon hanta mai tsanani.

Kara karanta wannan

Kamar Akulki: Yar Najeriya Da Ke Aiki A Dubai Ta Yi Bidiyon Dakin Da Take Rayuwa Da Gadaje Irin Na Yan Makaranta

“Wani matashi ya je siyan abinci ba tare da sanin cewa mai abinci ya yi amfani da paracetamol wajen gamsuwa da rayuwar cakin ba yanzu gashi a asibiti yana fama da ciwon hanta saboda bai san a ina ne abun ya faru ba.”
Dr. Egbema ya yi kira ga hukumar kula da abinci fa magunguna ta kasa da ta zuba ido kan gidajen abinci a kasar don tabbatar da inganci da lafiyar abincin da mutane ke ci a kasar.
“Wannan ne dalilin da yasa muke bukatar NAFDAC ya tashi saboda daga cikin abun da kuke yi shine abinci da magani. Ku je gidajen abinci, ku kalli abun da suke ci sannan ku tabbatar da ganin cewa yana da ingancin da za a iya cinsa.”
A cewar wata shafin lafiya ta yanar gizo Patient.info, “fiye da mutum 150 ke mutuwa a duk shekara saboda shan paracetamol ba bisa ka’ida ba.
“Paracetamol shine maganin da aka fi sha fiye da ka’ida. Yana iya haifar da ciwon hanta a cikin yan kwanaki, duk da amfani da magungunan kare lafiyar hanta. Ciwon hanta na iya muni.”

Kara karanta wannan

Goro a miya: Gwamnoni sun taru a Aso Rock don tattauna batun tattalin arziki, Buhari bai halarta ba

Legit.ng ta nemi jin ta bakin wata ma’aikaciyar asibiti wacce ke da ilimin harhada magunguna mai suna Aisha Alhassan kan haka inda tace shakka babu yin Girki da magani koma wani iri ne yana da illa sosai.

Ta ce:

"Kowane magani yana narkewa zuwa wasu sinadarai daban-daban a cikin hanta wanda ke fita ta jiki daga bisani.
"Toh idan ka yi amfani da shi wajen girki, zai narke sannan ya hade da wasu sinadarai kamar irin su maggi da sauran kayan girki…yana iya haifar da wani hadadden sinadari wand aka iya zama illa ga jiki."

Da Izinin Allah Zan Fito Lafiya: Eedris Abdulkareem Yace Matarsa Ce Za Ta Bashi Kodarta

A wani labarin, a ranar Asabar, 13 ga watan Agusta ne, abokai da takwarorin shahararren mawakin Najeriya, Eedris Abdulkareem, suka taru don karraman shi, ayyukansa da kuma taimakawa wajen sanar da duniya halin rashin lafiya da yake ciki a yanzu.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Wani Direba Ya Ci Na Kare Bayan Ayarin Gwamna Sun Tare Shi Kan Karya Dokar Tuki

Eedris, ya samu yabo sosai daga mutane da dama da suka yi magana kansa a wajen taron da aka shirya don tunawa da shekarun da ya sadaukar wajen yin gwagwarmaya.

Mawakin wanda ke fama da rashin lafiya da ya shafi koda shima da kansa ya yi magana a wajen taron da aka shirya a saboda shi, yayin da ya yi godiya ga dukkan mutanen da suka taru don taya shi murna da kuma goya masa baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel