Gwamnatin Jigawa Ta Rufe Makarantu Yayin da Dalibai Ke Rubuta Jarabawa Saboda Fargabar Kai Hari

Gwamnatin Jigawa Ta Rufe Makarantu Yayin da Dalibai Ke Rubuta Jarabawa Saboda Fargabar Kai Hari

  • Gwamnatin jihar Jigawa ta garkame makarantu saboda aukuwar wasu hare-haren 'yan bindiga a yankunan jihar
  • Wasu dalibai sun makale yayin da suka gaza kammala jarrbawarsu, suna jiran iyaye su zo dauke u bayan rufe makaranta
  • An sha rufe makarantu a jihohin Arewa sakamakon hare-haren da 'yan ta'adda ke kai wa mazauna

Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta ba da umarnin rufe dukkan makarantun gwamnati da ke jihar nan take bisa fargabar hare-haren da ake kaiwa makarantu a fadin jihar.

An rufe makarantun ne ba zato ba tsammani a ranar Laraba 17 ga watan Agusta yayin da daliban ke gudanar da jarrabawar kammala karatunsu.

Rufewar ta haifar da firgici da tsoro a tsakanin mazauna garin da dalibai. Da yawa daga cikin daliban sun makale, suna jiran a kwashe su daga garin.

Kara karanta wannan

Ruwa Yayi Awon Gaba da Dalibai 4 Dake Bidirin Kammala WASCCE a Gabar Teku

Rashin tsaro ya sa an garkame makarantu a jihar Jigawa
Gwamnatin Jigawa Ta Rufe Makarantu Yayin da Dalibai Ke Rubuta Jarabawa Saboda Fargabar Kai Hari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kakakin ma’aikatar ilimi ta jihar, Wasilu Umar, ya tabbatar wa Premium Times rufe makarantun, amma ya ki yin karin bayani.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amma wani shugaban makarantar firamare a daya daga cikin makarantun da ke Dutse, babban birnin jihar, ya shaida cewa:

“An bukaci mu rufe mu sallami daliban nan take.
“Dalibai har yanzu ba su gama jarrabawar Kimiyya da Ilimin Addinin Musulunci (IRK) ba kuma an ce su tafi.
“Rufewar ba ta da iyaka har sai baba ta gani. Mun yi imanin cewa hakan ya faru ne saboda tabarbarewar tsaro a jihar.”

Har ila yau, daya daga cikin daliban makarantar Sakandare ta gwamnatin Nuhu Sanusi, ya shaida cewa an bukaci su tafi ba tare da karbar takardar shaidar kammala karatun su da aka ce za a ba su gobe ba.

Dalilin rufe makarantun

Kara karanta wannan

An yi Shahada Yayin da Ruwa Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 50 a Kauyuka

Lamarin ya biyo bayan harin da aka kaiwa jami’an shige da fice ne a makon jiya a karamar hukumar Magari da ke jihar.

A harin dai an kashe jami'i tare da jikkata wasu biyu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, Lawan Adam, ya ce rundunar ‘yan sandan jihar ba ta ba da umurnin rufe makarantun ba.

Hakazalika, har yanzu ma’aikatar ilimi ba ta yi wa rundunar 'yan sanda bayanin abin da ya kai ta ga yanke wannan shawarar ba.

Karin bayani na nan tafe..

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.